Araghchi : Ya kamata Duniyar Musulmi ta dauki mataki mai karfi kan Isra’ila
Published: 23rd, March 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran, Abbas Araghchi, ya yi kakkausar suka kan zaluncin da gwamnatin Isra’ila ke yi kan al’ummar Falasdinu da ba su da kariya a yankin Zirin Gaza, yana mai jaddada bukatar hadin kai da daukar matakin gaggawa na kasashen musulmi domin dakile wadannan laifuka.
Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan a ranar Asabar, inda ya bukaci kasashen musulmi a duk fadin duniya da su dauki kwararen matakai da hadin kai don tunkarar ta’addancin Isra’ila.
Araghchi ya yi nuni da yadda gwamnatin Isra’ila ta sake dawo da yakin da take yi na kisan kare dangi a kan Gaza tun ranar Talatar data gabata wanda ya keta yarjejeniyar tsagaita bude wutar da aka cimma a zirin.
Sabon farmakin Isra’ila ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da 1,000, akasari mata da yara, baya ga kusan mutane 48,000 da sojojin suka yi wa kisan kare dangi tun da farko.
A wani bangare na jawabin nasa, Araghchi ya yi tir da hare-haren wuce gona da iri da Amurka da Birtaniya ke yi kan kasar Yemen, inda ya bayyana irin asarar da aka yi a tsakanin mata da kananan yara da ba su ji ba ba su gani ba, da kuma lalata kayayyakin more rayuwa na kasar.
Ya jaddada nauyin daya rataya a wuyan al’ummar musulmin duniya na tallafa wa ‘yan uwansu a wannan kasa ta Larabawa mai fama da tashe-tashen hankula da talauci.
A nasa bangaren, Yarima Farhan ya nanata matsayar Riyadh na yin Allah wadai da mummunan zaluncin gwamnatin Isra’ila, Ya kuma jaddada wajabcin hada kai da hadin gwiwa a tsakanin kasashen yankin don hana barkewar rikicin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
MDD da EU sun yi tir da wargaza yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Isra’ila ta yi
Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai sun ce, tsagaita bude wuta nan take a Gaza ya zama dole.
Da yake magana a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, mataimakin babban sakataren majalisar kan harkokin siyasa Khaled Khari, ya ba da rahoto game da tabarbarewar al’amura a Gaza bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni da aka kwashe kusan watanni biyu ana aiki da ita.
“A kowace rana, muna kara nisa daga manufar mayar da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su zuwa gidajensu lami lafiya,” in ji Khari, yayin da yake magana kan fursunonin Isra’ila da aka yi garkuwa da su a Gaza.
Babban jami’in kula da harkokin siyasa na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a dawo da tattaunawar tsagaita bude wuta da kuma kai kayan agaji a Gaza ba tare da wata tangarda ba.
Ya yi ishara da jawabin da babban jami’in agaji na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher ya yi wa UNSC a farkon wannan makon, inda yace yin aiki da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ita ce hanya mafi dacewa domin kare fararen hula a Gaza, da kuma sako wadanda aka yi garkuwa da su, gami da shigar da kayan agaji da kayayyakin bukatar rayuwa zuwa Gaza.
Khari ya ce jami’an MDD shida na daga cikin daruruwan mutanen da aka kashe tun bayan da Isra’ila ta sake dawo da kai hare-hare a ranar Talata.
A daya bangaren kuma Majalisar Tarayyar Turai ta yi Allah wadai da “rugujewar yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwa da jikkatar fararen hula masu yawa a hare-haren jiragen saman Isra’ila a baya-bayan nan”.
Har ila yau, ta bukaci komawa ga aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta nan take, tare da jaddada wajabcin ci gaba zuwa mataki na biyu na yarjejeniyar wanda Isra’ila ta yi fatali da shi.
Majalisar EU ta ce aiwatar da yarjejeniyar na da matukar muhimmanci wajen ganin an sako dukkan wadanda ake tsare da su a Gaza da kuma gidajen kurkukun Isra’ila, tare da cimma nasarar kawo karshen fada na dindindin.