A tattaunawarsa da Aminiya wani manomin gurjiya, Malam Muhammad Dahiru Kanda ya bayyana cewa, ya shafe sama da shekara 25 yana noman gurjiya ba tare da ya taba samun wani tasgaro ba.
Ya kara da cewa, shi noman gurjiya na da muhimminci matuka domin kuwa yana samar wa duk mai yin sa babbar riba.
Mata sun ƙwace kasuwancin kayan lambu a Gombe Mutumin da girgizar ƙasa ta razana ya shekara 2 yana zaune a cikin kogoA cewarsa, noman gurjiya noma ne da bai sai ka tanadar masa babbar gona ba, ya danganta ne ga yadda duk ka dauke shi, amma kuma ko da rabin hekta ka dauka, ka noma, matukar ka gyara ta to kuwa ko tantama babu in Allah SWT Ya so za ka same ta a yalwace.
Haka nan in har ya kasance ka samu kasar noma mai kyau kuma mai karfi za ka samu alheri sosai wajen samun biyan bukata.
A cewarsa a duk shekara yakan samu buhunhuna biyar zuwa 7 na gurjiya a ‘yar karamar gonarsa da ba ta kai eka guda ba, wadda wannan gurjiya in ya samu yakan biya bukatunsa da na iyalansa.
Ya ci gaba da cewa, noman gurjiya na bukatar hakuri da kuma shuka ta a kan lokaci daidai da lokacin da aka fara shuka gyada domin kuwa ita gurjiya kamar gyada ce, tana bukatar shiga cikin kasa tunda ‘ya’yanta a cikin kasa take zuba su.
Haka kuma, noman gujiya in son samu ne, ka kebance mata wurinta daban komai kakantarsa, maimakon ka shuka ta cikin gero ko dawa ko kuma hada ta cikin gyada domin in ka kebance wajen shuka ta daban, takan fi haihuwa da yawa sabanin shuka ta hade da wasu amfanin gona, kana tana bukatar a dan sa takin gida ko na zamani.
Don haka a gaskiya noman gujiya na da matukar muhimmanci domin kuwa yakan samar wa manoma alherin da ba ya misaltuwa, musamman ganin cewar gurjiya na da matukar daraja a kasuwa.
A yanzu haka buhun gurjiya mai nauyin kilo 50 kudinsa ya kai kimanin Naira dubu 55 zuwa dubu 60.
Baya ga haka kuma akwai bukatar manomi in ya zo shuka gurjiya, ya zabo iri mai kyau ba irin da zai tsumbure ba domin samun yalwarta.
“Yin hakan na daga cikin abin da ke taimaka min da ma sauran manoma wajen samun gurjiya mai yawa in lokacin cire ta ya yi, kuma matukar manomi na son amfana da ita a kaka, to kuwa ya guji yawan cire ta da danyentakarta tun ba ta kai ga kosawa ba, don sayarwa.
Sai dai in ba bukatar hakan ne ta taso ba, domin ni sau tari nakan hakura ne da cirar ta in tana danya illa daga lokaci zuwa lokaci nakan cira don kai wa iyali su dafa, su ci.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gurjiya noman gurjiya
এছাড়াও পড়ুন:
MDD Ta Bukaci Taimako Dangane Rikicin Sudan Wanda Ya Isa Kasar Chadi
Shugaban hukumar yan gudun hijira na MDD Filippo Grandi wanda ya ziyarce sansanonin yan gudun hijira na kasar Sudan a Chadi ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen duniya su taimaka don kula da bukatun yan kasar sudan wadanda suke gudun hijira a kasar Chadi.
Grandi ya kara da cewa akwai bukatar agaji da gaggawa zuwa kasar Chadin da kuma sauran kasashen da suke daukar nauyin yan gudun hijira na sudan. A halin yanzu dai ana ganin mutane kimani 20,000 ne suka rasa rayukansu, sannan wasu da dama suka ji rauni sannan wasu kuma suka zama yan gudun hijira.