Ɗan sa-kai ya kashe matasa biyu a Borno
Published: 23rd, March 2025 GMT
An kama wani jami’in rundunar sa-kai ta JTF, Modu Mallam Gana mai shekaru 27 a garin Monguno, bisa zarginsa da harbin wasu gungun matasa wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu tare da raunata daya.
Wata majiyar leƙen asiri ta shaida wa Zagazola Makama cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:15 na safiyar ranar 21 ga Maris, 2025, a lokacin da wasu matasa suka tsaya a gaban ofishin dakarun da ke Unguwar Bakin Kasuwa, a Karamar Hukumar Monguno.
Majiyar ta ce wanda ake zargin Modu Mallam Gana ya harzuka da tsayarwar matasan a bakin ofishinsu, lamarin da ya bude musu wuta.
Wadanda abin ya shafa — Ya’zainab Bum da Goni Mohammed Ahmadu — sun mutu nan take yayin da Hamsatu Ali ta samu munanan raunuka kuma aka kwantar da ita a babban asibitin Monguno.
Sai dai an tabbatar da mutuwar Ya’zainab Bum da Goni Mohammed Ahmadu, inda aka mika wa iyalansu gawarwakinsu domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada yayin da Hamsatu Ali tana kwance a asibiti tana jinya.
Majiyar ta ce an kama wanda ake zargin nan take, kuma aka mika shi ga ‘yan sanda don gudanar da binciken da ya dace da shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: jihar Borno
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Kama Wasu Da Ake Zargin Ɓarayin Wayar Wutar Lantarki Ne A Yobe
Rundunar ‘yansandan jihar Yobe ta kama wasu mutane biyu da ake zargin barayin wayar wutar lantarki ne a Damaturu babban birnin jihar. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa, rundunar ‘yansanda ta Karasuwa ce ta kama wadanda ake zargin – Yahaya Mustapha, 28, da Bello Yakubu, 38, da misalin karfe 1:00 na rana a ranar 12 ga watan Afrilun 2025. ‘Yansanda Sun Gano Haramtaccen Wurin Haɗa Makamai A Kano Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutum Ɗaya A Bauchi, Wasu Sun Jikkata Abdulkarim ya ce, wadanda ake zargin sun fito ne daga unguwar Takari da ke karamar hukumar Gashua Bade a jihar, an kama su ne da manyan igiyoyin wutar lantarki a kauyen Waro da ke karamar hukumar Karasuwa. A cewar sanarwar, an kama wadanda ake zargin ne a lokacin da suke loda igiyoyin a kan keke-napep mai kafa uku. Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Emmanuel Ado ya jaddada kudirin rundunar na yaki da masu aikata miyagun laifuka da barnata dukiyoyin jama’a, inda ya bukaci jama’a da su sanya ido tare da kai rahoton duk wasu zarge-zarge ko wasu mutane da ke shirin barnata kadarorin jama’a. Ya kuma yabawa ‘yan jihar bisa yadda suke bayar da sahihan bayanai, wanda hakan ya taimaka wajen bunkasa kokarin rundunar.Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp