Aminiya:
2025-04-14@17:04:46 GMT

Yadda garin Zip ya nutse a Kogin Binuwai

Published: 23rd, March 2025 GMT

Wani abin al’ajabi da ban tsoro ya auku inda rana tsaka garin Zip da ke Jihar Taraba ya nutse baki dayansa a cikin Kogin Biniwai.

Wakilin Aminiya ya ziyarci garin domin gani da ido, inda ya ruwaito cewa a halin yanzu babu sauran wani gini ko bishiya da ake gani a garin, duk kogin ya hadiye su, sun nutse a cikin ruwa.

Ɗan sa-kai ya kashe matasa biyu a Borno Mahaifiyar Gwamnan Katsina ta rasu

Garin na Zip da ke Karamar Hukumar Karim-Lamido ta Jihar Taraba yana bakin Kogin Biniwai ne, kuma mafi yawan mazaunansa masunta ne da manoma.

Sun kuma bayyana wa wakilinmu yadda abin ya faru da yadda suka tsallake rijiya da baya da irin asarar da suka tafka da kuma halin da ibtila’in ya jefa su a halin yanzu.

Wani mazaunin garin, Alhaji Gambo Sa’idu, wanda kuma dan uwan sarkin garin ne, ya shaida wa wakilinmu cewa, a gidansa akwai dakuna fiye da takwas kuma gidan nasa kamar sauran gidajen garin duk sun nutse a cikin Kogin Biniwai.

Yadda abin ya faru

Ya kara da cewa tun a shekarun baya ne al’ummar garin suka fara ganin gine-ginen da suke bakin gabar kogin garin sun fara tsagewa, daga bisani wasu suka fara ruftawa suna fadawa cikin kwaryar kogi.

Alhaji Gambo ya ce, “Tsohon Sarkin Zip, Marigayi Alhaji Uba Sa’idu ya kai rahoto ga Karamar Hukumar Karim-Lamido da kuma Gwamnatin Jihar Taraba kan yadda gidaje ke ruftawa suna ta fadawa cikin ruwa, amma babu wanda ya zo ya duba abin dake faruwa.”

Kwatsam ƙasa ta fara motsi gidaje na ruftawa

“A cikin daminar da ta wuce ne kawai al’ummar garin suka ga wasu sassan garin na motsi sai kuma gine-gine suka fara darewa.

“Da muka ga kasa tana motsi gine-gine kuma suna darewa sai muka shiga kwashe iyalanmu da kayayyakinmu daga cikin gidajenmu domin gudun kada gidajen su rufta cikin ruwa da iyalanmu da kayayyakinmu.

“A cikin wannan yanayin gine-gine da suke cikin garin dukkansu suka rufta cikin ruwa kuma ruwa da yashi suka rufe garin baki daya,’’ in ji shi.

Ruwa ya haɗiye gine-gine

Ya ci gaba da cewa “In ba wanda ya san dama akwai gari a wajen ba, babu wanda zai taɓa cewa akwai gari a can baya kafin wannan lamari ya faru, ba za a taba cewa akwai gari a nan ba.

“Ga inda garin Zip yake can ruwa da yashi sun rufe shi, abu daya ne ake gani, shi ne rodin da aka yi amfani da su wajen gina masallacin Juma’a, su ne kadai ba su nutse a cikin yashi baki daya ba,’’ in ji Gambo.

Gidana ta nutse a ruwa – Malam Bashiru

Malam Bashiru Gambo shi ma mazaunin garin na Zip ne, ya shaida wa wakilin Aminiya cewa ya kashe kudi kimanin Naira miliyan bakwai wajen gina gidansa mai dakuna shida a lokacin da kayan gini ke da arha.

Ya ce gidan nasa dungurumgum ya nutse a ruwa, amma dai Allah Ya taimake shi iyalinsa sun tsira, in banda wasu kayayyakinsa da suka nutse a ruwa.

A cewarsa, idan zai sake gina gida kamar nasa a yanzu, to zai kashe kudi fiye da Naira miliyan goma sha biyar saboda tsadar kayan gini.

Iyalai sun koma zama a bukkoki

Magidancin ya ce yanzu shi da iyalinsa da sauran mutanen sun koma zama a cikin bukkoki da suka yi na ciyawa saboda ba su da kudin da za su sake gina wasu gidaje.

Malam Bashiru ya ce, “Masallacin Juma’a da makarantar firamare da asibiti da kuma coci kamar sauran ginegine da ke garin duk sun rufta a cikin ruwa.

“Yanzu masallacin Juma’a da ciyawa aka yi shi, sa’annan kuma yaranmu ba sa zuwa makaranta domin har yanzu ba a sake gina wata makaranta a garin ba, kuma mata masu juna biyu da kananan yara ba sa samun kula ta fuskar kiwon tafiya.

“Abin mamaki shi ne yanzu ba wani taimako da mu al’ummar wannan gari muka samu daga Gwamnatin Jihar Taraba kuma yanzu ga shi lokacin damina na kara gabatowa,’’in ji Bashiru.

Mijina ya kamu da rashin lafiya – Hussaina

Wata matar aure mai ’ya’ya takwas mai suna Malama Hussaina Muhammed ta shaida wa wakilin Aminiya cewa da kyar ta tsira tare da mijinta da ’ya’yanta a lokacin da garin ya nutse a ruwa.

Ta ce duk da cewa sun tsira, amma a sanadiyyar wannan matsalar mijin nata, Malam Muhammed ya sami rashin lafiya, wanda a yanzu haka ya bar garin Zip ya koma wani gari ya bar ta da ’ya’yanta suna zaune a ’yan bukoki.

Malama Hussaina ta ce katifunsu da wasu kayayyaki duk sun nutse a ruwa kuma tana cikin halin kaka-ni-ka-yi domin mjiiin nata ya bar ta ita kadai kuma ’ya’yan nata kanana ne.

Kamar girgizar kasa

Shi ma Malam Ya’u Baba Tsoho, ya ce ba su taba fuskantar irin wannan ibtila’in ba, duk da kasancewar garin na Zip ya dade.

Ya ce, “Za a iya danganta hatsarin da ya auku a garin da cewa girgizar kasa ce domin a ranar da lamarin ya faru, garin ya motsa kuma gine-gine suka dare kuma dukkan gidajen suka yi ta ruftawa cikin kogi har da bishiyoyi ma da ke ciki da kewayen garin na Zip, duk sun nutse a cikin ruwa.”

Babu dauki daga gwamnati

Ya ce, “A can baya lokacin da jama’ar garin suka ga ginegine na tsagewa sarkin garin, Marigayi Uba Sa’idu ya kai rahoto ga Karamar Hukumar Karim-Lamido da kuma Gwamnatin Jihar Taraba har ma da hotuna, amma babu abin da hukumomin Jihar Taraba suka yi har ya zuwa lokacin da garin baki daya ya rufta a cikin ruwa.

“Har zuwa yanzu babu wani jami’in gwamnatin Jihar Taraba ko kuma na Karamar Hukumar Karim-Lamido wanda ya ziyarci garin domin ganin abin da ya faru, kai ma da kanka ka ga inda tsohon garin yake, ruwa da yashi sun rufe garin baki daya, ba wani alamar gini ko bishiya, kuma a yanzu duk al’ummar garinmu a bukoki muke zaune,’’ in ji Ya’u.

Mista Micah Dantala lsoko, wanda shi ne Magatakardan Sarkin Zip, ya shaida wa Aminiya cewa duk gine-ginen da ke garin sun nutse a cikin ruwa wanda haka ya haifar wa da jama’ar garin asarar dukiya mai yawan gaske.

Ya bayyana cewa Masallacin Juma’a da coci da makarantan firamare da asibiti suna daga cikin gine-ginen da suka nutse baki daya a cikin kogin na Biniwai.

Ya ce har yanzu babu wani dauki da aka kawo wa jama’ar garin don a tsusayawa.

“Mun yi sa’a ba a samu asarar rai a laokacin wannan hadari ba, amma daukacin gine-ginenmu da kayayyakimu duk sun nutse a cikin ruwa yanzu kusan duk al’umma suna zaune tare da iyalansu a dakunan ciyawa domin kayan gini sun yi tsada sosai,’’ in ji Micah.

Shi ma Sarkin garin na Zip, Malam Yusuf Babatato, ya bayyana cewa al’ummar garin sun yi asarar daukacin gidajensu da wuraren kasuwanci da masallatai da coci da makarantar firamare da asibiti.

Ya ce, “Kamar yadda duk wanda ya zo nan zai gani, kusan dukkan jama’a dakunan ciyawa suke zaune tare da iyalinsu.”

Shirin gina sabon gari ya samu cikas

Malam Yusuf Babatato, ya ce a halin yanzu sun sami wani wuri nesa da tsohon garin da ya nutse a ruwa za su gina sabon gari, amma matsalar kudi ta kawo jinkiri wajen fara aikin.

Ya ce, “Babbar matsalar da ke damun al’ummar garin ita ce rashin makaranta da asibiti domin sai an tafi wurare masu nisa ake samun kulawa ta fuskar kiwon lafiya, yara kuma suna zaune ba sa zuwa makaranta domin har yanzu ba a sake gina wata makaranta ko asibiti a garin ba.”

Duk kokarin da wakilin Aminiya ya yi domin jin ta bakin Kwamishinar Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Taraba, Hajiya A’isha Barde, ya ci tura domin ba ta amsa kiran waya ba.

Wakilin namu ya tura mata rubutaccen sakon waya, inda ta dawo masa da amsar cewa ba ta sami labarin abin da ya auku a garin na Zip ba. Sai dai kuma ba ta yi wani bayani game da ko akwai wani mataki da gwamnatin Jihar Taraba za ta dauka kan lamarin ba, har zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoton.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Binuwai Jihar Taraba Karamar Hukumar Karim Lamido sun nutse a cikin ruwa al ummar garin nutse a ruwa garin na Zip Jihar Taraba

এছাড়াও পড়ুন:

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 108

108-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani  mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin Rumi, ko kuma cikin wasu littafan. Da fatana masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///.. Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan lamami na biyu daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s) kuma da na farko ga Fatimah (s) diyar manzon All..(s).

A cikin shirimmu da ya gabata mun kawo maku yadda Khalifa Uthman ya tura walidu dan Ukuba dan Abu muid a matsayin walin Kufa, mun kuma ji irin barnan da yayi, da baitul malin musulmi, ya sha giya ya bada sallar Asubaha, raka’o’ii 4 sannan ya juya yace in kara maku ne.

Banda haka, yana yayi aman giyar a cikin masallaci, sannan yana sanya zoben zinari wanda aka haramtawa mazaje sanya shi. Har’ila yau munji yadda Khalifa Uthman bai ji dadin wadanda suka kawo kararsa daga kufa ba, sai da suka sami mafaka wajen Amirul muminina,(a) wanda ya yiwa Khalifa magana a kansa, sannan ya amince ya tube shi ya kuma dawo da shi Madina, aka tabbatar da shaidar cewa ya sha giya, amma an kasa samun wanda zai yi masa haddi, saboda kusancinsa da Khalifa, sai Imam Ali (a).  Wanda ya tashi ya dauko bulala ya kuma tsaida haddin All..a kansa.

Sannan mun yi yadda manzon All..(s) ya bada umurnin a kashe baban Walid bayan an kamashi cikin fursinonin da aka kama a Badar, saboda tufa yawun da ya yi a furkar manzon All..(s) a Makka, sannan ya zage shi. Sannan mun ji cewa All..ya sauko da yar Alkur’ani mai girma yana kiran walid dan Ukba a matsayin fasiki, saboda kariyar da yayiwa manzon All..(s) dangane da da Banu Mustalak.

Don haka mukace saboda wannan da kuma wasu abubuwa bai kamata a ce irin wannan mutum ya zama shugaban al-ummar musulmi musamman manya-manyan garuruwan da suke da baki sabbin musulunta wadanda suke bukatar ilmin addinin da halaye masu kyau a wajen shuwagabannin musulmi don su koyi addinin musulunci su kuma iya rikeshi ba. Koma wadanda basu musulunta daga cikinsu su musulunta ba.

Daga nan sai Khalifa ya nada Sa’id dan Ass a matsayin gwamnan Kufa, shima daga cikin dangin Uthman, kuma shi yaro ne matashi wanda, yake cikin bai da kamun kai, don haka ne ma, mutanen Kufa, bayan sun je cewa Khalifa ya aiko Sa’ida dan Ass a matsayin walin kufa sun taru sun hana shi shiga garin. Sai dai daga bayan an fi karfinsu, inda khalifa ya bada umurni a koresu daga Kufa zuwa sham, wajen Mu’awiya dan Abi Sufyan, sun je mu’awiya ya basu masaiki mai kyau kuma yana kola da su tare da kokarin janra’ayinsa su mika kai ga banu Umayya, amma bayan wani lokaci ya ga cewa ba wani ci gaba, kuma zamansu a sham ma zai iya zama hatsari gareshi. Sai ya rubuta Khalifa Uthman kan cewa ba zai iya ci gaba da ajiyesu a sham ba.

Khalifa ya sake maida su Kufa wajen Sa’id dan Ass, sai wata rana sa’ida ya tare mutane a kasar Azumi ya ce masu wa yaga wata sai wani sahabi mai suna Hashin dan Utmah, ya ce ya gaba wata, sai sa’id ya ce masa da wannan idonka da baya gani ne ka ga watan ?.

Sai Hashim, ya ce, masa kana aibatani da wannan idan, an ji mani ciwo ne a idon kan tafarkin All.. a yakin Yarmuk ne ya rasa idonsa guda. Don haka Hashim ya ta shi da safe ba tare da azumi ba, yayi sallah, sai mutane da dama suka sha ruwa saboda ya ce ya gani, don shi ba makaho ne kwata-kwata ba. Kuma manzon All..(s) ya ce ” Ku yi azumi da gani ku kuma ajiye azumi da ganin jinjirin wata.

A lokacinda Sa’id ya ji cewa Sa’id yayi salla kuma mutane da dama sun bishi, sai ya sa aka kama shi aka kawo shi gidan sa,  ya sa aka dakeshi aka kuma kona gidansa.  A cikin wannan halin sai Malik dan Ashtar daya daga cikin shuwagabannin kabilun yemen a Kofa ya ji sa’ida yana cewa: A dukiyar kufa gaba daya mallakin shi da kuma banu Umayya ne.

Sai ta tashi yayi masa inkari, sannan malamai da mahaddatan alkur’ani a Kufa sun goyi bayansa. A lokacinda dogarin sa’id ya ga haka, sai yah au kansu, suka taru suka yi masa duka har ya suma.

A nan sai Sa’id ya rubuta wasika zuwa ga Khalifa Uthman wanda ya bada umurnin a koresu daga Kufa zuwa Sham, wanda muka yi magananrsa a baya.

Bayan da mu’awiya yak asa zama da su ne sai Khalifa ya ce Sa’id ya koresu zuwa Khum na kasar ta sham amma karkashin Abdurrahman dan Khalid bin Walid sai suka koma Khums , Abdurrahman ya wahalar da su so sai.

Sai suka fadawa Abdurrahman ya nemammasu Afwa daga Uthman a lokacinda ya yi masu fawa suka koma kufa sai suka sake fitowa zuwa Madina inda suka bukaci Uthman ya tube masu sa’id ya ki yin haka, sai Sa’idu ya Je madina don wata bukatarsa, zai sake komawa Kufa sai Malik da sauransu suka ce ba zai sake komawa Kofa ba, suka zare takubbansu, sai dai a yi yaki. Don haka ala tilas Uthman ya tube shi ya aiko masu da wani.

Haka ma a Basra, Uthman ya tube Abu Musa Al-ashari ya maye gurbinsa da wani matashi dan kawwar mahaifiyarsa, Abdullahi dan Amiru wanda baifi shekaru 25 a duniya ba.

Mutanen Basra sun yi ta korafi amma ya ki ya cire shi. Ya ci gaba da kasancewa walin Basra har zuwa lokacinda ya ji labarin an kashe Uthman ya yawushen baitul  Mali ya arce zuwa Makka, inda ya hadu da A’isha da Talha da Zubair, har zuwa lokacinda suka Imam Ali (s) ya yake su a Basra ya kuma sami galaba a kansu.

04-Mu’awiya dan Abisufyan, wanda ya kasance dan Abu sufyan, kuma gwamna a kasar sham tun lokacin Khalifa na biyu. A cikin sirar Khalifa Umar yakan sanya gwamnoni ko wali a yankunar daular musulunci ya kuma tubesu tare da karamin laifi ko kuma babu wani laifin da suka yi, sai idan ya ga dama sai ya saukesu kawai.

Amma tunda ya dora mu’awiya kan kasar sham bai tabe shi ba, banda haka yana kara masa karfi.

Tun lokacinda ya dorashi kan aiki a kasar sham da urdon bai sauke shi ba. Sannan idan wani ya kawo masa sukansa, na cewa yana al-mubazzaranci, yana sanya rigunan da suka haramta a musulunci, sai Khalifa Umar yace: Ai wannan hi ne kisran musulmi.

Khalifa Umar yakan yi hisabiwa gwamnoninsa a ko wace shekara, sannan yakan raba dukiyoyin biyu ya dauki rabi ya maida shi madina, wannan dukiyoyin da suka samu ta hanyar Halar wato ta kasuwanci ko kuma, wasu hanyoyin da suka dace.

Amma banda  mu’awiya dan Abusufyan, shi yana kashe kudade jama’a yana rayuwa irin ta sarakuna, amma sai ya rufe idanunsa  kamar bai gani ba. Wannan halin haka ya tafi har ya bar duniya.

Sannan a lokacinda zai rasu, khalifa Umar ya fadawa wadannan mutane 6 wadanda yace manzon All..(s) ya rasu yana mai yarda da su kan cewa, idan sun ta hasada a tsakaninsu, sun rigima a tsakaninsu, to mu’awiya zai yi maganinsu.

Wannan ya nuna cewa sun shirya Mu’awiya a kasar Sham ne don ya zama Khalifa, a wani lokaci nan gaba. Ko kuma ya kwace khalifanci, daga khalifa a Madina, ya maida ita cikin bani Umayya wadanda suka yaki manzon All…(s) har zuwa Fatahin Makka. Kuma abinda ya faru kenen bayan shahadar Amirul Mumimnina (a).

Don mu’awiya ya yi karsfi a kasashen shammat guda 4, siriya lebanin Urdun da Falasdin, sannan a likacin Uthman ya karawa mu’awiya wasu yankuna kamar Khums. Don haka sojojinsa sun fi karfin sojojin da zasu fito daga Madina in da za’a yi yaki ne a tsakaninsu. Sannan ga duniya ga kuma biyya wanda mutanen sham suke masa. Basa saba masa, suna sonsa yana sonsu, basu san wani musulunci bas ai wanda Mu’awiya dan abi Sufyan ya fada masu. Daga cikin ya fada masu cewa Aliyu dan Abitalib (a) bayan sallah. A lokacinda suka ji labari an kashe shi a masallaci yana bada sallah, sai suka ce, shin yana sallah ne?.

Don haka bayan kissan khalifa na biyu, Sai aka zabi Uthman a matsayin Khalifa a bayansa, ya tabbatar da mu’awiya a matsayinsa tunda shi dangin Banu Umayya ne, don haka, na gida ne ya sami iko, ya zama khalifa. Don haka bamu taba jin wani sabani tsakanin mu’awiya da khalifa Uthman ba, har aka kashe shi bayan shekaru kimani 12 da Khalifanci. Banda haka a lokacin Khalifancinsa yak ara karfafa shi kamar yadda muka fada.  

Don haka zamu iya cewa ba wanda ya sami rabo mai tsoka daga cikin dangin Banu umayya daga wajen Khalifa Uthman kamar yadda Mu’awiya ya samu. Don a lokacinda yake mulkin kasar sham kamar sarki ne mai zaman kansa. Daga lokacin Khalifa Umar har zuwa kissan Khalifa Uthman, mu’awiya ya yi kimani shekaru 20 yana sarauta a Sham.

Don haka ba sai mun yawaita magana a kansa a yanzu, ba, sai nan gaba, a lokacinda Imam Ali ya zama Khalifa sannan mu’awiya yace ba zai yi masa bai’a ba. Da kuma abubuwa da suka biyu baya, har ya kwace iko da Imam Hassan (a).

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shrimmu na yau sai kuma wata Fitowa idan All..ya kaimu wassalamu a laikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Bello Turji ya kashe manoma 11 a Sakkwato
  • Hukumar OCHA Ta Bayyana Cewa Yahudawan Sahyoniyya Sun Ninninka Ayyukan Korar Falasdinawa A Yamma Da Kogin Jordan
  • Jiragen Saman Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Luguden Wuta Kan Asibitin Baptist Da Ke Gaza
  • Dagewa Iran Takunkuman Zalunci Na Daga Cikin Manufofin Tattaunawa Da Amurka: Aref
  • Kallo Daya Mutum Za Yi Min Ya Gane Masana’antar Kannywood Ta Canza Rayuwata -Farida Abdullahi
  • Yadda Rashin Ilimi Ke Cutar Da Rayuwar Al’umma
  • Yadda Ake Tuwan Amala Da Miyar Uwaidu
  • Yadda bom ya tashi da ɗan gwangwan a Legas
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 108
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassa Al-Mujtaba (a) 107