Aminiya:
2025-04-14@16:13:25 GMT

Matasa sun kashe yaron da suka yi garkuwa da shi a Bauchi

Published: 23rd, March 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta kama wasu matasa huɗu da ake zargi da yin garkuwa da kuma kashe wani yaro ɗan shekara shida, Shuaibu Safiyanu, a ƙauyen Sade da ke Ƙaramar Hukumar Darazo.

Aminiya ta ruwaito cewar mahaifin yaron, Safiyanu Abdullahi ne, ya sanar da Sarkin garinsu, Musa Isah, cewa a ranar 20 ga watan Maris, 2025, ɗansa ya ɓace.

Ɗan sa-kai ya kashe matasa biyu a Borno Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da shirin noman rani na Lallashi

Washegari, wani ya kira shi a waya yana neman kuɗin fansa.

Da farko, ya nemi miliyan uku (₦3,000,000), amma daga baya suka rage zuwa Naira dubu ɗari biyu (₦200,000).

A ranar 21 ga watan Maris, aka gano gawar yaron a cikin daji, an ɗaure masa wuya da igiya.

Nan take aka kai shi asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Daga nan aka bai wa iyalansa gawarsa domin yi masa jana’iza.

Kakakin ’yan sandan Jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce bayan samun rahoton lamarin, jami’an su suka fara bincike.

Sun fara binciken ne daga wajen POS da ke kusa da inda aka buƙaci a biya kuɗin fansar.

A yayin binciken, sun kama wani matashi mai shekara 23, Rabi’u Muhammadu daga ƙauyen Leka.

An gano cewa lambar wayarsa ce aka yi amfani da ita wajen kiran mahaifin yaron.

Sannan ’yan sanda sun gano asusun bankin da aka bayar don biyan kuɗin fansar: Lambar asusu: 0145285130 Sunan mai asusu: Ozochikelu Samson Banki: Union Bank PLC

Bayan kama Rabi’u, ya bayyana cewa Samson Ozochikel, mai shekara 35 daga ƙauyen Sade, shi ne ya shirya yadda za a sace yaron.

Ya kuma ambaci wasu matasa biyu, Muhammad Sani (Jingi), mai shekara 25, da Musa Usman (Kala), mai shekara 30, dukkaninsu daga ƙauyen Leka.

A halin yanzu, ’yan sanda suna tsare da su, kuma ana ci gaba da bincike a sashen binciken manyan laifuka (SCID).

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, ya tabbatar da cewa za su tabbatar da an yi adalci.

Ya kuma roƙi jama’a da su ci gaba da bai wa ’yan sanda haɗin kai, tare da sanar da su duk wani abun zargi ta layin kiran wayar gaggawa 112 ko Police Control Room a lamba 08156814656.

Rundunar ta jaddada ƙudirinta na kare rayuka da dukiyar al’ummar jihar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Garkuwa yaro mai shekara

এছাড়াও পড়ুন:

Zulum Ya Gana Da Yaron Da Aka Ci Zarafi, Ya Ba Shi Gida, Tallafin Karatu

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji Sun Ceto Fasinjoji 16 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Filato
  • ’Yan bindiga sun kashe mutane 40 a sabon hari a Filato
  • Rigima: Mawaƙi Portable ya kwana a hannun ’yan sanda
  • Zulum Ya Gana Da Yaron Da Aka Ci Zarafi, Ya Ba Shi Gida, Tallafin Karatu
  • An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen Filato
  • An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Gwaska da mayaƙa 100 a Katsina
  • Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro
  • Mahaifi ya yi wa ’yarsa ciki a Bauchi
  • NIMASA Za Ta Adana Wa Nijeriya Dala Biliyan 400 A Shekara Daga Cazar Kudaden Safarar Kaya
  • An kashe mutum kan zargin satar kare a Bauchi