Aminiya:
2025-04-14@16:57:45 GMT

An shiga ruɗani yayin da Sanusi II da Bayero ke shirin hawan salla a Kano

Published: 23rd, March 2025 GMT

Al’ummar Jihar Kano, sun shiga shida ruɗani yayin da rikicin Masarautar jihar, ya ɗauki wani sabon salo game da shirin gudanar da bikin hawan salla.

Tsagin sarakunan jihar na 15 da na 16, wato Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero, sun shirya gudanar da hawan salla duk da shari’ar da ke gudana kan rikicin masarautar.

Matasa sun kashe yaron da suka yi garkuwa da shi a Bauchi Mata sun ƙwace kasuwancin kayan lambu a Gombe

Lamarin ya ɗauki sabon salo ne, bayan wata wasiƙa daga Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya fitar kan shirinsa na yin hawan salla a bana.

Wasiƙar, wacce sakataren Sarkin, Abdullahi Haruna Kwaru, ya sanya wa hannu, an aike wa Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, inda ya bayyana shirinsa na gudanar da hawan salla.

Daga cikin hawan da ya bayyana cewar zai yi akwai Hawan Daushe, da Hawan Nassarawa a ranakun 2 da 3 ga watan Shawwal 1446 bayan hijira.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya umarci Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, da ya fara shirin gudanar da hawan salla.

A cikin wasiƙarsa, Aminu Ado, ya ce wannan hawan na da muhimmanci a gare shi saboda zai cika shekarj biyar da zama sarki.

An jima ba a gudanar da bikin hawan salla ba a Kano saboda fargabar abin da ka iya faruwa tsakanin mabiyan sarakunan biyu.

Rikicin ya fara ne bayan da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya tuɓe Sanusi II daga sarauta, tare da naɗa Aminu Ado a matsayin Sarkin Kano.

Sai dai a shekarar 2024, Majalisar Dokokin Kano, ta sake sauya dokar masarautar tare da rushe dukkannin masarautu biyar da Ganduje ya ƙirƙira, tare da mayar da Sanusi II a matsayin Sarki.

Wannan ya janyo ce-ce-ku-ce da tashin hankali a jihar, lamarin da ya sanya tsagin Aminu Ado tafiya kotu.

Kotu ta yanke hukuncin cewa komai ya ci gaba da zama a yadda yake har zuwa lokacin da Kotun Ƙoli za ta yanke hukuncin ƙarshe, lamarin da ya sa dukkanin ɓangarorin biyu ke iƙirarin suna da iko a kan sarautar.

Har yanzu, gwamnatin Kano da Sanusi II ba su ce komai ba kan wasiƙar da Aminu Ado, ya aike wa ’yan sanda, kuma har yanzu ba a ji ta bakin rundunar ’yan sandan jihar ba.

Sai dai, jama’a na nuna damuwa kan abin da ka iya faruwa.

Malam Haladu Bello, wani dattijo mai shekaru 78 a duniya, ya bayyana damuwarsa kan cewa lamarin zai iya haifar da rikici.

“Na sha ganin hawan salla mai ƙyatarwa da kuma wanda ke da matsaloli, amma wannan yana da ban tsoro.

“Abin takaici ne yadda shugabanninmu ke watsi da hatsarin da jama’a ke fuskanta.”

Wani matashi mai shekaru 30, Alhaji Usman Shehu, ya bayyana cewa wannan rikicin cikin gida ne, ba wai abu ne da zai sa mutane cikin fargaba ba.

Ya ce: “Kullum cikin fargabar abin da zai biyo baya muke. Wannan ba daidai ba ne. A bar mu, mu more al’adunmu cikin zaman lafiya.”

Yayin da bikin salla ke ƙara ƙaratowa, al’ummar Kano na ci gaba da fargabar abin da ka iya faruwa idan duka sarakunan biyu suka ci gaba da shirinsu na gudanar da hawan salla.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Aminu Ado Bayero Fargaba gwamna hawan salla Rikicin Masarauta Ruɗani gudanar da hawan salla a gudanar da

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya kaddamar da aikin sake gyaran titin Abuja zuwa Kano

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya kaddamar da aikin sake gyaran babban titin Abuja-Kaduna-Zariya-Kano, wadda ke da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin Arewacin Najeriya.

Da yake jawabi a taron kaddamarwar a Kagarko, Jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani, ya bayyana yadda aka yi watsi da hanyar da kuma irin mummunan tasirin da hakan ya yi ga rayuka da ci-gaban tattalin arziki.

Gwamna Uba Sani, ya yaba wa Tinubu bisa farfado da aikin, yana mai nuni da muhimmancin hanyar a matsayinta na mafi yawan zirga-zirgar ababen hawa a Arewa.

Da yake ba da tabbacin kamma aikin a cikin watanni 14, Tinubu wanda Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya ce za a gina titin ne da kankare, kamar babbar hanyar Legas zuwa Kalaba.

An kama kwayoyin N300m da mutane 650 a Kano An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar Edo Badaƙalar Miyagun Ƙwayoyi: Kotun Amurka ta ba da umarnin fitar da bayanai kan binciken Tinubu

Ministan ya kara da cewa aikin zan dangana har zuwa filin jirgin sama na Kano, kuma za a sanya kyamarorin CCTV gaba daya a tsawon titin, wanda sabon dan kwangila ne zai aiwatar.

Ya ce, shugaban kasa ya amince da naira biliyan 252 don muhimman sassan aikin, inda aka riga aka biya kashi 30%, yanan mai yaba muhimmiyar rawar da Gwamna Uba Sani ya taka a aikin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Kaddamar Da Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” Na Harshen Vietnam
  • Iran Ta Ce Za’a Gudanar Da Zagaye Na Gaba Tsakaninta Da Amurka Ne A Birnin Roma Na Kasar Italiya
  • Tinubu ya kaddamar da aikin sake gyaran titin Abuja zuwa Kano
  • Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya
  • Al’ummar Mauritaniya Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Nuna Adawa Da Yakin Gaza
  • An kama kwayoyin N300m da mutane 650 a Kano
  • An kama miyagun kwayoyin N300m da mutane 650 a Kano
  • Isra’ila ta yi barazanar fadada hare-hare Gaza yayin da ta yanke Rafah daga birnin Khan Yunis
  • An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano
  •  A Yau Asabar Ne Ake Bude Tattaunawa A Kasar Oman Akan Shirin Makamashin Nukiliyar Iran