Tunanin Raya Al’ummar Dan Adam Zai Tabbatar Da Makoma Mai Haske Ga Kowa
Published: 23rd, March 2025 GMT
Kimanin shekaru 12 da suka wuce, wato a ranar 23 ga watan Maris din shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da tunanin raya al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya, a karon farko, yayin da yake jawabi a wata jami’a dake birnin Moscow na kasar Rasha. Asalin tunanin ya shafi al’adun gargajiya na kasar Sin, wanda ya bukaci a samu jituwa, da daidaito tsakanin al’ummu daban daban, da tsakanin dan Adam da muhallin halittu.
Bisa tushen tunanin raya al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya ne, kasar Sin ta gabatar da karin shawarwari, irinsu Ziri Daya da Hanya Daya, da wadanda suka shafi kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arziki, da tsaro, da cudanyar al’adu a duniya, ta yadda za a samu damar aiwatar da tunanin a harkokin dan Adam na fannoni daban daban.
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya taba nanata cewa, yayin da ake aiwatar da tunanin raya al’ummar dan Adam, ba za a ce wasu al’adu sun fi wasu ba, kuma ba za a nemi maye gurbin wani tsarin al’umma da wani na daban ba. Maimakon haka, abin da za a yi shi ne hakuri da bambancin kasashe daban daban, ta fuskokin tsarin al’umma, da al’adu, da matsayin ci gaban tattalin arziki, sa’an nan a raba riba, da hakki, da nauyin aiki a tsakanin su, don tabbatar da makoma mai haske ta al’ummar dan Adam. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: al ummar dan Adam
এছাড়াও পড়ুন:
Fadar Mulkin Amurka: Tattaunawa Da Iran Ta Yi Armashi
Fadar mulkin Amurka ta “White Hosue” ta bayyana cewa tattaunawar da aka yi a tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci da wakilin Donald Trump akan gabas ta tsakiya Steve Witkoff, ta hanyar shiga tsakanin kasar Oman, ta yi armashi.
Da marecen jiya Steve Witkoff ya bayyana cewa; shugaba Donald Trump ya ba shi umarnin ya yi duk abinda zai iya domin rage tazarar sabanin da ake da ita ta hanyar tattaunawa da diflomasiyya.
Bayanin na fadar mulkin Amurka ya kuma yaba wa kasar Oman wacce ta kasance mai masaukin baki na tattaunawar da aka yi wacce ba ta gaba da gaba ba ce a tsakanin Amurkan da kuma Iran.
Gabanin bayanin na fadar mulkin Amurkan, manzon musamman na shugaba Donald Trump, Steve Witkoff ya fada wa tashar talabijin din NBC cewa, ya yi tattaunawa mai matukar armashi da kuma amfani.
Tun a ranar Asabar da safe ne dai ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci ya isa birnin Mascut, inda ya gana da takwaransa na kasar Sayyid Hamad Bin Hamud al-Busa’idi, tare da mika masa bayanai da su ka kunshi mahangar Iran akan tattaunawar.
Ministan na harkokin wajen Oman ya zama mai shiga tsakanin kasashen biyu a tsawon lokacin tattaunawar. Bangarorin biyu sun yi musayar takardu har sau hudu.
A ranar Asabar mai zuwa ne dai za a ci gaba da tattaunawar daga inda aka tsaya a wani wurin da ba a kai ga ayyana shi ba.