’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara
Published: 23rd, March 2025 GMT
Aƙalla jami’an rundunar tsaron al’umma ta Zamfara (CPG) 10 ne, suka rasu, yayin da wasu 14 suka jikkata a wani hari da ’yan bindiga suka kai musu a yankin Anka da ke Jihar Zamfara.
Sun kai harin ne a ranar Asabar bayan da jami’an tsaro suka kai farmaki wani sansanin ’yan bindiga da ke dajin Bagega a ranar Juma’a da Asabar.
A yayin farmakin, sun kashe ’yan bindiga da dama kuma sun kuɓutar da wasu mutanen da aka sace a sansanin wani ƙasurgumin shugaban ’yan bindiga, Alhaji Beti.
Wata majiya ta bayyana cewa jami’an tsaro sun kuma ƙone gidan wani shugaban ’yan bindigar mai suna Bellon Kaura, wanda lamarin da ya fusata su.
“Kurakuran da suka yi shi ne komawa ta hanyar da suka bi a lokacin farmakin farko,” in ji wani shugaba a yankin Anka.
“’Yan bindigar sun tsere daga sansaninsu amma sun shirya tarko, sun yi kwanton-ɓauna, kuma suka buɗe wuta bayan jin ƙarar baburan jami’an tsaron.”
Harin ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro bakwai daga Anka da kuma uku daga Talata Mafara.
Sunayen waɗanda suka rasu sun haɗa da Shehu Lawali, Murtala Mesin, Ubandawaki Moda, Muhammad Want, Haruna Kwanar Maje, Ibrahim Ware Ware, Yusuf Ware Ware, Rabi’u Barbara, Lawali Dan Hassi Jangebe, da Badamasi Gima.
An yi jana’izarsu a Anka a ranar Lahadi, inda Gwamna Dauda Lawal ya halarta, tare da ɗaukar alƙawarin ci gaba da goyon baya wajen yaƙi da ’yan bindiga a jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga hari Jami an Tsaro kwanton bauna Zamfara jami an tsaro yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
UNICEF: Yara a Gaza suna fama da matsalar kwakwalwa da ba a taba ganin irinsa ba
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya sanar da cewa, yara a Gaza suna fuskantar matsakar kwakwalwa da ba a taba ganin irinsa ba a kan kananan yara.
“Ba mu da wani bayani a tarihin wannan zamani dangane da ke bukatar tallafin lafiyar kwakwalwa kamar yaran Gaza,” in ji mai magana da yawun UNICEF James Elder a wani taron Majalisar Dinkin Duniya a Geneva.
Sannan kuma jami’in ya yi Allah wadai da tauye hakkin yara da ake yi da gangan a Gaza, ya kuma bukaci masu karfin fada a ji a duniya da su dauki mataki.
Ya kara da cewa an toshe alluran rigakafi 180,000 na rigakafin yara masu mahimmanci, da na’urorin saka jariran da ba su kai ga lokacin haihuwa ba, inda Isra’ila ta hana shigar da wadannan kayayyakia cikin yankunan zirin gaza.
Babban jami’in na UNICEF ya ce, daukar irin wadannan matakana kan yara yana a matsayin babban laifi wanda ka iya zama laifin yaki bisa dokoki na kasa d akasa.
A kan haka ya kara jaddada kiransa ga kasashe masu karfin fada a ji da su sauke nauyin da ya rataya a kansu kan batun Gaza.