Gobara ta tashi a gidan mai sakamakon fashewar tanka a Neja
Published: 24th, March 2025 GMT
Wata tanka ɗauke da man fetur ta kama da wuta yayin da ta ke sauke mai a gidan mai na A.A. Rano da ke Kontagora, a Jihar Neja.
Lamarin ya faru ne da da misalin ƙarfe 7 na daren ranar Lahadi kusa da Asibitin Gaba.
Gwamnonin Arewa sun yi wa Radda ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a ZamfaraShaidu sun ce gobarar ta fara ne yayin da ake sauke man fetur, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba kasancewar sauran tankunan mai maƙare suke da fetur.
Jami’an kashe gobara sun garzaya wajen don shawo kan lamarin, amma har yanzu wutar na ci gaba da yaɗuwa.
“Babu wanda aka ruwaito ya rasa ransa, amma mutane sun tsere domin tsira da rayukansu,” in ji wani mutum, mai suna Abba Mohammed.
Ƙoƙarin jin ta bakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, ya ci tura zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: A A Rano Gobara Kontagora
এছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila ta yi barazanar fadada hare-hare Gaza yayin da ta yanke Rafah daga birnin Khan Yunis
Isra’ila ta ce ta karbe iko da wata muhimmiyar hanya a zirin Gaza a wani mataki da ya yanke gaba daya yankin kudancin Rafah mai yawan jama’a daga sauran yankunan Falasdinawa da aka yiwa kawanya.
A cikin wata sanarwa da Isra’ila ta fitar yau Asabar ta ce dakarunta sun yi wa Rafah kawanya gaba daya tare da samar da “yankin tsaro” a can.
Sanarwar da ministan harkokin soji na gwamnatin Isra’ila Katz ya fitar ta ce sojojin sun karbe ikon “Morag axis, wanda ke ratsa Gaza tsakanin Rafah da Khan Yunis.”
Katz ya kuma yi kira ga Falasdinawa da su fara kaura zuwa yamma, yana mai gargadin cewa nan ba da jimawa ba za a kara kaimi da fadada ayyukan soji zuwa wasu yankuna a cikin mafi yawancin Gaza.
IDF ta ce ta karɓe da abin da ta bayyana da cibiyar tsaronta da ta yi wa laƙabi da ”Lungun Morag”, sunan wani ginin da Isra’ila ta taɓa yi tsakanin biranen biyu.
A yanzu haka sojojin Isra’ila na gina titi a wurin, da nufin samar da wani wuri da Isra’ila ke iko da shi da ya raba Zirin Gaza.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Hamas ke cewa ta aika wakilanta zuwa Masar domin tattaunawa da masu shiga tsakani kan yiwuwar dawo da yarjejeniyar zaman lafiya.