Masanin Amurka: Matakan Kariyar Cinikayya Da Amurka Ke Aiwatarwa Babban Kuskure Ne
Published: 24th, March 2025 GMT
A yau Lahadi, kwararren masanin tattalin arziki dan kasar Amurka Jeffrey Sachs ya bayyana cewa, matakan kariyar cinikayya da Amurka ke aiwatarwa babban kuskure ne.
Jeffrey wanda ya halarci dandalin bunkasa kasa na Sin na shekarar nan ta 2025 a birnin Beijing, ya kara da cewa Amurka na kara karkata ga salon kariyar cinikayya karkakin manufofinta na tattalin arziki.
Ya ce Amurka na ingiza salon rufe fasahohinta, yayin da Sin ke kara gabatarwa duniya da fasahohin ci gaba. Dukkanin wadannan na nufin Sin za ta zamo mai cin gajiya daga bunkasar tattalin arzikin duniya a shekaru masu zuwa. Daga nan sai mista Jeffrey ya nuna damuwa game da halin da Amurka ke ciki, yana mai cewa manufofin gwamnatin Trump ba su da ma’ana ga Amurka ita kan ta da ma duniya baki daya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kiyaye Ci Gaba Mai Dorewa A Huldar Sin Da Amurka Ya Dace Da Moriyar Sasssan Biyu
A yau Litinin ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun, ya jagoranci taron manema labarai na yau da kullum, inda wani dan jarida ya yi tambaya game da ko Sin za ta shiga tattaunawa da Amurka, game da hakan Guo Jiakun ya ce, a ko da yaushe kasar Sin na da imanin cewa, kiyaye zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da ci gaba mai dorewa a dangantakar Sin da Amurka, ya dace da moriyar jama’ar kasashen biyu, da kuma fatan al’ummomin duniya baki daya.
Dangane da rikicin Ukraine kuwa, Guo Jiakun ya ce a baya-bayan nan, kungiyar “Kawancen zaman lafiya” kan rikicin Ukraine ta gudanar da wani taro a birnin New York, domin tattauna halin da ake ciki game da rikicin Ukraine, da kuma fatan samun dauwamammen zaman lafiya.
Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasashen duniya, wajen taka rawa mai ma’ana, don cimma nasarar warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp