Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya yi kira ga kasashen duniya da su kawo karshen rikicin da Isra’ila ke ci gaba da haifarwa a yankin gabas ta tsakiya.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, Araghchi ya yi Allah wadai da sabbin hare-haren da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza tare da hana kai agajin jin kai a yankin  a matsayin keta haddin yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta watan Janairu.

Ya kuma yi kira da a dauki matakin gaggawa a duniya kan yadda Isra’ila ke ci gaba da ruruta wutar rikici a yankin baki daya.

Isra’ila ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023, amma ta kasa cimma manufofinta da ta ayyana kan yakin, duk da kashe Falasdinawa 50,000 galibi mata da kananan yara, tare da jikkata wasu fiye da 113,213.

Gwamnatin mamaya ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta amince da shirin tsagaita wuta da kungiyar gwagwarmayar Hamas a  Gaza, wadda aka fara aiki da ita a ranar 19 ga watan Janairu.

Bayan shudewar watanni biyu da fara aiwatar da yarjejeniyar, Isra’ila ta sa kafa ta yi fatali da ita, kuma ta ci gaba da kaddamar da hare-haren kisan kiyashi a kan al’ummar Gaza

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Isra ila ta da Isra ila

এছাড়াও পড়ুন:

Uwargidan Shugaban Kasar Sin Ta Tattauna Da Takwararta Ta Kasar Kenya

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta Bukaci Kasashen Indiya Da Pakistan Da Hada Kai Don Yakar Ta’addanci
  • Sojojin Mamaya Sun Yi Kasan Kiyashi A Zirin Gaza Da Kuma Ci Gaba Da Killace Falasdina  Cikin Masifar Yunwa
  • Gwamnan Babban Bankin Sin: Harajin Amurka Ya Jefa Kasuwanni Da Kasashe Masu Tasowa Cikin Hadari
  • Rasha Ta Fara Aika Isakar Gas Zuwa Kasar  Iran Ta Azarbaijan Don Sayarwa A Kasuwannin Duniya
  • Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Yi Gargadin Munanan Sakamakon Da Zai Biyo Bayan Kashe Falasdinawa
  • Shugaban Amurka Ya Ce: Natenyahu Ba Zai Hadi Fada Da Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ba
  • Sharhin Bayan Labarai: Shin Kissan Mutanen Gaza Gaba Daya
  • Faransa ta jaddada aniyarta na ci gaba da tattaunawar nukiliyar iran
  • Uwargidan Shugaban Kasar Sin Ta Tattauna Da Takwararta Ta Kasar Kenya
  • Sojan HKI Ya Halaka A Gaza