Wata mata ta haifi jaririn da ba nata ba
Published: 24th, March 2025 GMT
Wata mata mai suna Krystena Murray ’yar Amurka, wadda ta ɗauki ciki tare da haife jariri namiji ba tare da sanin cewa ba ɗanta ba ne, ta fara ɗaukar matakin shari’a a kan wani asibitin da ke taimaka wa mata samun ciki ta hanyar dashen ɗantayi (IBF).
Matar tana zargin asibitin da yi mata dashen ɗantayin da ba nata ba, bayan an tilasta ta, ta mayar wa asalin iyayen jaririn ɗansu.
Krystena Murray, mazauniyar Jihar Georgia, ta ɗauki cikin ne bayan dashen ɗantayi na (IBF) da aka yi mata a asibitin masu neman haihuwa da ake kira Coastal Fertility Clinic, a watan Mayun 2023.
To amma daga baya an gano cewa, ɗantayin da ta rena a cikinta na wasu ma’auratan ne daban, kamar yadda majiyar BBC ta ruwaito. Hakan ya fito fili ne bayan da Murray ta haifi jaririn da bai yi kama da ita ko wanda ya ba ta gudumawar maniyyi ba.
Duk da haka, Madam Murray ta so a bar mata yaron, don ta ci gaba da renon sa har tsawon watanni, amma hukumomi suka bai wa ainahin iyayen dan ikon karɓen ɗansu.
A cikin wani bayani da ta sanar ta hannun lauyanta, Murray ta ce: “Na ɗauki jaririn nan a cikina, na kamu da son sa, na haife shi, sannan na shaƙu da shi sosai, irin shaƙuwa ta ɗa da uwa, amma yanzu an ƙwace shi. Ba zan taɓa fita daga wannan takaici ba.”
Murray wadda baturiya ce, ta haifi jaririn, wanda ya kasance baƙar fata a watan Disamban 2023.
Ta ƙi sanya hotunan jaririn a shafukan sada zumunta sannan ta ƙi bari ’yan uwa ko abokanta su gan shi.
Daga nan ne ta sayi abin gwajin gano halittar gado, wanda za ta iya yin gwaji a gida.
Sakamakon da ta samu a watan Janairun 2024 ya tabbatar mata cewa, jaririn ba shi da alaƙa da ita, kamar yadda ta bayyana a koken da ta rubuta a kan asibitin.
Bayan wata ɗaya, ta sanar da asibitin game da lamarin. Asibitin ya sanar da asalin iyayen jaririn, waɗanda su kuma suka kai ƙara domin karɓar ɗan nasu, lokacin da yake da wata uku a duniya.
Dole ta sa Murray ta miƙa jaririn bayan lauyoyinta sun tabbatar mata cewa, ba za ta samu nasara ba, idan ta je kotu da nufin a bar mata jinjirin.
A halin yanzu jaririn na hannun iyayensa na asali a wata jiha, inda suka sauya masa suna. Koken da Murray ta shigar ya bayyana cewa, har yanzu ba ta san ko asibitin Coastal Fertility ya bai wa wasu nata ɗantayin ne ko kuma a’a.
A wani saƙo da ya tura wa kafar talabijin ta CBS News, asibitin ya amince cewa, ya tafka kuskure, sannan ya nemi afuwa game da halin da ya jefa matar a ciki.
“Wannan ne kuskure ɗaya da muka yi, kuma bai shafi wasu mutanen da muka bai wa kulawa ba,” kamar yadda asibitin ya sanar a bayaninsa.
“A ranar da aka gano wannan kuskuren, mun sake yin nazari mai zurfi a kan ayyukanmu tare da ɗaukar matakan kariya domin kare masu zuwa neman magani a wurinmu ta yadda ba za a sake samun irin haka ba.”
A shekarun baya-bayan nan an shigar da ƙararrakin asibitocin maganin haihuwa da dama kan yin kuskure wajen dashen ɗantayin.
Dashen IBF wani tsari ne da ake haɗa ƙwan haihuwar mace da maniyyin namiji a kwalba kafin a dasa ɗantayin a cikin mahaifar mace domin reno a matsayin juna-biyu.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An Kashe Shanu 36, an ba 42 guba a Filato
Shanu 36 sun mutu baya ga wasu 42 da ake zargin an ba su guba guba a kusa da yankin mahaɗar Tafi Gana a Ƙaramar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.
Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) a Karamar Hukumar Bassa, Ya’u Idris, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yamma lokacin da shanun ke kiwo a yankin.
Ya’u ya ƙara da cewa an sanya guba ne a cikin gauta, waɗanda aka warwatsa a kewayen wurin kiwon kuma shanun suka ci.
Ya ci gaba da cewa sun kai rahoton lamarin ga dukkan hukumomin tsaro ciki har da Hukumar DSS, da ’yan sanda, ya kuma Babban Kwamandan Rundunar ta kuma din ya ziyarci wurin da abin ya faru.
Wannan lamarin ya faru ne kwanaki biyu kacal bayan wani mummunan hari a kauyen Zikke, a cikin wannan ƙaramar hukumar ta Bassa, inda aka kashe mutane 52 tare da jikkata wasu da dama. An kuma kona gidaje da dama a harin.
Mazauna yankin da aka kai harin sun zargi makiyaya da hannu a kashe-kashen da aka yi a ranar Litinin, zargin da makiyayan suka musanta.
Kakakin rundunar tsaro ta Operation Safe Haven, Manjo Samson Zhakom, bai amsa saƙon da wakilinmu ya aike masa ba game da lamarin a lokacin da ake rubuta wannan rahoto.
A sakamakon ƙaruwar rashin tsaro, Gwamna Caleb Mutfwang a ranar Laraba ya haramta kiwon dabbobi da daddare, da kuma jigilar shanu da hawa babura bayan ƙarfe 7 na yamma. Wannan matakin na daga cikin hanyoyin da gwamnatin jihar ta ɗauka domin hana ci gaba da samun sabani tsakanin makiyaya da manoma.
Gwamnan, a cikin wani jawabi da ya yi wa al’ummar jihar a ranar Laraba, ya bayyana cewa a makon da ya gabata, an kai hari kauyen Zikke inda aka kashe mutane da dama.
Sai dai, wannan dokar ta haifar da ce-ce-ku-ce, musamman ma daga direbobin manyan motocin da ke Jos, waɗanda suka bayyana haramcin jigilar shanu bayan karfe 7 na yamma a matsayin wanda ya ci karo da wata doka da ta riga ta hana zirga-zirgar manyan motoci tsakanin karfe 6 na safe zuwa 9 na yamma. Sun kuma roƙi gwamnatin da ta sake duba wannan doka.
Haka kuma, kungiyar MACBAN ta nuna damuwarta game da wannan doka, inda ta bayyana cewa lokacin da aka ƙayyade zai iya shafar rayuwar makiyaya, musamman wadanda za su iya kasancewa tare da shanunsu a kasuwanni bayan karfe 7 na yamma.
Sun cewa suna goyon bayan dokar domin tabbatar da zaman lafiya, amma suna roƙo gwamnan da ya ɗaga lokacin zuwa karfe 8 na dare domin mutanensu su samu damar komawa gida lafiya.
Laifin gwamnatocin baya ne — GadgiA nasa ɓangaren, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Pankshin Kanke da Kanam a Jihar Filato, Yusuf Adamu Gagdi, ya bayyana cewa abin takaici ne yadda yankunan da suka yi fice wajen noma a Bokkos, Bassa, Wase, da Mangu suka zama filin daga.
Ya zargi gazawar gwamnatocin baya wajen ba kama shugabannin hukumomin tsaro da laifin gazawarsu wajen samar da tsaro a yankunansu da ta haifar da karuwar matsalar tsaro a kasar.
Gadgi ya kuma alaƙanta ƙaruwar hare-hare a Filato da tserewar da ’yan bindiga ke yi daga jihohi Zamfara da Sakkwato zuwa dajin Filato sakamakon ragargazarsu da sojoji suka tsananta.
Za mu dawo da zaman lafiya — ’yan sandaMataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda (DIG) Kwazhi Bzigu Dali ya ziyarci yankunan da aka kai hari domin tantance halin da ake ciki, inda ya gudanar da sintiri ta sama da ƙasa tare da ganawa da shugabannin ƙananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya kuma tabbatar wa mazauna yankin da cewa Sufeto-Janar na ’Yan Sanda ya ƙudiri aniyar dawo da zaman lafiya, inda ya sanar da tura karin jami’an tsaro da kayan aiki.
Dattawan Arewa sun fusataƘungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta yi kakkausar suka ga kashe-kashen da ake yi a Filato, inda ta bayyana su a matsayin abin kunya ga ƙasa.
Sun soki rashin ɗaukar mataki da Gwamnatin Tarayya ke yi, suna masu kira da a tura jami’an tsaro da kayan aiki nan take tare da tabbatar da an yi adalci.
Haka kuma, Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta nuna baƙin cikinta game da sake ɓarkewar rikicin a Filato, inda ta yi kira ga shugabannin al’umma da na addini da su tallafa wa Gwamna Mutfwang wajen kwantar da hankula da kuma gina zaman lafiya mai ɗorewa.
Gwamnatin Tarayya ta sake nanata ƙudirinta na kawo ƙarshen rashin tsaro a faɗin ƙasar, inda ta bayyana ƙoƙarin da ake yi na ƙarfafa tsaron kasa.
Tsohon ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya yi kira ga gwamnatin da ta daina magana ta fatar baki kawai, ta ɗauki matakai na zahiri don kare ’yan Najeriya.