Ƴansandan Sun Gayyaci Sanata Karimi Kan Zargin Shigar Kungiyar Leƙen Asirin Rasha Majalisa’
Published: 24th, March 2025 GMT
Ƴansandan sun gayyaci Sanata Sunday Karimi domin bayani kan zarginsa na cewa ƙungiyar leƙen asirin ƙasar Rasha ta KGB ta samu shiga cikin Majalisar Dokoki, wanda ke barazana ga tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya.
Zargin ya samo asali ne daga rahoton da Sanata Karimi ya raba akan ƙungiyar ta WhatsApp a Majalisar Dattijai a ranar 23 ga Fabrairu, 2025.
A cikin ƙarar da ta fitar a ranar 5 ga Maris, 2025, Sanata Akpoti-Uduaghan ta nuna damuwa kan wannan batu, tana bayyana cewa irin wannan zargi yana ɗauke da barazana mai girma ga tsaron ƙasa da kuma buƙatar gaggawar yin bincike. Ta yi kira da cewa wannan batu ba za a iya watsar da shi ba, domin ya shafi dimokuraɗiyya da tsaron ƙasa.
Sanata Karimi, wanda aka gayyace shi don yin ƙarin bayani kan rahoton da ya yaɗa, zai yi amsa tambayoyi a shalƙwatar ‘Yansanda a Abuja a ranar 24 ga Maris, 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Me Ya Janyo Jifan Mawaka A Arewacin Nijeriya?
Lamarin ya faru ne a lokacin da matashin mawakin yake kan dandamali ya na rera daya daya daga cikin fitattun wakokinsa, har zuwa lokacin wannan rahoto, Bilal Billa bai fitar da wata sanarwa a kafafen sadarwar ba, amma kuma faruwar lamarin ya janyo cece kuce inda wasu a bangare guda ke ganin abin da aka yi wa mawakan ya yi daidai yayin da wasu kuma ke ganin hakan bai dace ba.
Wasu na ganin cewar kalmar nan ta bahaushe da ya ce “Bokan Gida Bai Ci”, shi ne ke faruwa a kan wadannan mawakan, wasu kuma na ganin wannan wata hanya ce da aka dauko domin dakile tauraruwarsu da ke haskawa, wasu kuma ke cewa wannan kawai wata hanyar nuna hassada ce da mutanen arewacin Nijeriya ke amfani da ita saboda a kudancin kasar irin wannan ba kasafai yake faruwa tsakanin mawaka da sauran al’umma ba.
Ko ma dai minene dalilin da ya janyo jifar mawakan, ba zai rasa nasaba da banbancin ra’ayi ba kokuma rashin jituwa a tsakanin mawaka da masu saurarensu akan wani abinda su ka taba fafi ko aikatawa a cikin wakokinsu, sau da dama mawakan siyasa na fuskantar wannan kiyayya daga masoyansu wadanda ra’ayinsu ya saba a siyasance.
A wani lokaci can baya shahararren mawakin siyasa a Nijeriya Alhaji Dauda Adamu Kahutu wanda aka fi sani da Rarara ya fuskanci kalubale daga mutane da suke da banbancin ra’ayin siyasa, har ta kai ga wasu fusatattun matasa sun farmaki ofishinsa domin nuna fushi a kan wakokin suka ko tsangwama da yake yi wa gwaninsu a siyasance.
Amma kuma ba kasafai ake samun mawakan nanaye, nishadi ko soyayya da samun tsama tsakaninsu da masoyansu ba, duba da cewar mafi yawan lokutan mawakan kan sosa masu inda yake yi masu kaikayi a fagen soyayya, amma kuma wadannan al’amura da su ka faru a wannan shekarar ya jefa tambaya a zukatan wasu da dama a kan MI YA JANYO JIFAR MAWAKA A AREWACIN NIJERIYA.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp