NDLEA Ta Kama Ƴar Indiya Ɗauke Da Hodar Iblis A Kano
Published: 24th, March 2025 GMT
Hukumar yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta kama wata mata ‘yar ƙasar Indiya mai suna Neetu Neetu, mai shekara 42, a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano, ɗauke da hodar iblis mai nauyin kilo 11 da aka ɓoye a cikin ledojin da ke kama da kwallon alawar cakulati. An cafke ta ne a yayin binciken shigowarta daga jirgin Qatar Airways daga Bangkok ta Vietnam da Doha.
Shugaban hukumar, Birgediya Janar Buba Marwa (Rtd), ya ce wannan kamun ya sake nuna yadda masu safarar kwayoyi ke amfani da ‘yan ƙasashen waje don kutsawa da miyagun kwayoyi cikin ƙasar. A cewarsa, NDLEA na ci gaba da daƙile irin wannan yunƙuri ta hanyar bayanan sirri da fasahohin zamani.
NDLEA Ta Gargadi Iyaye Kan Bayyanar Alawar Ƙwaya A Kano Jami’an NDLEA Sun Kashe Budurwa A Kano, An Damƙe SuA wani sumame a Kano, an kama Michael Ogundele dauke da tramadol guda 50,000 da aka boye a cikin bututun gas, yayin da a Gunduwawa aka cafke Sunday Ogar da kilogram 27 na wiwi. Haka zalika, an kama Khadijah Abdullahi a Lungun Bulala da kwalabe 424 na maganin tari mai sinadarin Kodin.
A Lagos kuwa, jami’an NDLEA sun kama mutane da dama da wiwi, da tramadol, da Kodin a Mushin, Apapa da Ikotun. NDLEA ta ci gaba da shirinta na wayar da kai a faɗin ƙasar, ciki har da makarantu da masallatai. Marwa ya yaba wa jajircewar jami’an hukumar, yana mai kira da su ci gaba da aiki da kwazo da rikon amana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Matasa Sun Daka Wawasu Kan Tirelar Kayan Agajin Ramadan Na Seyi Tinubu A Gombe
Shirin ya fuskanci suka sosai a shafukan sada zumunta, inda suke ganin cewa, Arewa ta cancanci kulawa fiye da haka, yayin da wasu kuma ke ganin tallafin ya dace.
A wani faifan bidiyo da Daily Trust ta gani, an ga wasu fusatattun matasa suna kwashe kayan abinci a wata babbar mota da aka ajiye a bakin titi.
An ga matasan suna jefo kayan ga wadanda suke kasa domin tattarawa musu, sannan suka yi awon gaba da kayayyakin.
Abubuwan da ke cikin Tirelar sun haɗa da shinkafa, sukari, man girki, gishiri da taliya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp