Aminiya:
2025-03-25@20:53:13 GMT

Juventus za ta sallami kocinta Thiago Motta

Published: 24th, March 2025 GMT

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus na shirin raba gari da mai horas da ’yan wasanta, Thiago Motta, yayin da ko kaka ɗaya bai cika ba a kwantaragin da ya ƙulla da ƙungiyar ta Italiya.

A cewar Jaridar wasanni ta La Gazzetta dello da Gidan Talabijin na Sky Sport, Juventus na shirin maye gurbin Thiago Motta da tsohon ɗan wasan ƙungiyar, Igor Tudor.

Fursunoni 12 sun tsere bayan fasa gidan yari a Kogi Za mu farfaɗo da Madatsar Ruwa ta Biu — Zulum

Juventus dai za ta ɗora wa sabon kocin nauyin jajircewa wajen ganin ƙungiyar ta ƙare a cikin sahun huɗun farko na teburin Gasar Serie A ta bana, domin samun damar buga Gasar Zakarun Turai a kaka mai zuwa.

A halin yanzu ƙungiyar da ke fama da rashin kuɗi, ita ce ta biyar a teburin Serie A yayin da ya rage sauran wasanni 9 a ƙarƙare gasar.

Kafofin watsa labarai daga Italiya sum ruwaito cewa nan da kowane lokaci ƙungiyar za ta sanar da raba gari da Thiago Motta mai shekaru 42 da kuma naɗa magajinsa, Igor Tudor.

A watan Yulin bara ne dai Thiago Motta ya karɓi ragamar jagorancin ƙungiyar bayan ya yi ƙoƙari matuƙa a ƙungiyar Bologna a kakar 2023/24.

Sai dai a yanzu duk gwiwowinsa sun yi sanyi sakamakon rashin kataɓus a ƙungiyar da ake yi wa laƙabi da Old Lady.

A ƙarƙashin jagorancin kociyan ɗan ƙasar Brazil, Juventus ta buga wasanni 42, inda ta yi nasara a 18 da canjaras 16 sai kuma rashin nasara a wasanni takwas.

A watan Fabrairun da ya gabata ne ƙungiyar PSV ta koro Juventus daga Gasar Zakarun Turai, sannan Empoli ta fatattako ta daga Kofin Italiya.

Wasanni biyu na bayan nan da Motta ya jagorancin ƙungiyar ta gamu da rashin nasara a hannun Atalanta wadda ta lallasa ta da ci 4-0 — wadda ita ce rashin nasara mafi girma da ta yi a gida tun 1967 — sai kuma kashi da ta sha a hannun Fiorentina da ci 3-0.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Mutane Miliyan 9 Na Iya Kamuwa Da Cutar HIV Saboda Rashin Tallafi

Sai dai duk da yaba wa Amurka bisa irin taimakon da ta bayar a baya, Byanyima ta nuna damuwa kan yadda aka dakatar da tallafin kwatsam ba tare da shiri ba.

Wannan na iya haddasa koma baya a ƙoƙarin da aka shafe shekaru ana yi na rage yawan masu kamuwa da cutar, musamman a yankunan da ke fama da talauci da ƙarancin kayan kiwon lafiya.

Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa, idan ba a samu sabbin hanyoyin tallafi ba, yiwuwar ƙaruwar mace-mace sakamakon cutar HIV na da matuƙar girma.

Hakan na iya rusa nasarorin da aka samu a yaƙin da duniya ke yi da cutar.

Ana ci gaba da kira ga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin agaji da su ceto shirin da ke kare miliyoyin rayuka daga barazanar cutar HIV.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ECOWAS Za Ta Yi Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafuwa
  • Mutane Miliyan 9 Na Iya Kamuwa Da Cutar HIV Saboda Rashin Tallafi
  • Juventus ta sallami kocinta Thiago Motta