Wajibcin Gina Al’ummar Duniya Mai Kyakkyawar Makomar Bai Daya
Published: 24th, March 2025 GMT
Al’ummar duniya mai kyakkyawar makomar bai daya na nufin makomar kowace al’umma da kowace kasa tana da nasaba da juna. Hakan na nufin ya kamata mu yi rayuwa tare duk rintsi duk wuya, muna more daukaka da wahala tare da kuma kokarin mayar da duniyarmu al’umma guda mai jituwa, inda za mu mai da burin mutane na samun ingantacciyar rayuwa ta zama gaskiya.
Tunanin al’ummar duniya mai kyakkyawar makomar bai daya shi ne ginshikin tunanin Xi Jinping kan harkokin diflomasiyya, wanda ke wakiltar zurfafa fahimtar kasar Sin game da muhimman dokokin dake kula da ci gaban zamantakewar dan Adam, kuma yake ba da amsa ta musamman ta Sinawa ga tambayar “Wace irin duniya ce ya kamata mu gina, kuma ta yaya za mu gina ta?” Tun farkon wannan zamani da muke ciki, wannan hangen nesa ya sauya daga shawarar kasar Sin zuwa yarjejeniya ta kasa da kasa, daga buri zuwa aiki na hakika, kuma daga faffadan ra’ayi na falsafa zuwa tsarin bayanai game da aiwatar da manufofi. Kana ya zama fayyatacciyar ka’idar zamaninmu, wanda ta shimfida hanyar hadin gwiwar duniya da gudanar da mulkinta. Har ila yau, gina al’ummar duniya mai kyakkyawar makomar bai daya na nufin yunkurin samar da kyakkyawar duniya mai cike da zaman lafiya, aminci, wadata, budaddiya, hadaka, da kuma tsabta. Kazalika ra’ayin yana kira da a samar da sabon tsarin gudanar da harkokin duniya bisa tuntuba, da ba da gudunmawar hadin gwiwa, da fa’idodi na bai daya, masu daukar dabi’un da suka dace da dan Adam. Yana kuma habaka sabon nau’in alakar kasa da kasa, ta hanyar kaddamar da shirin Raya Duniya, da shirin Tsaron Duniya, da shirin Wayewar Kai na Duniya dake aiki a matsayin ginshikan wannan tunanni. Haka ma hadin gwiwa mai inganci karkashin tsarin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya mai amfani wajen aiwatar da wannan hangen nesa, tana bai wa kasashe damar yin aiki tare wajen magance kalubalen duniya da samun wadata tare. Wannan hangen nesa a karshe yana jagorantar duniya zuwa ga makoma mai cike da zaman lafiya, tsaro, wadata da ci gaba. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: ummar Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Duniya na ci gaba da yin tir da Isra’ila kan dawo da hare-harenta a Gaza
Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai sun ce, tsagaita bude wuta nan take a Gaza ya zama dole.
Da yake magana a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, mataimakin babban sakataren majalisar kan harkokin siyasa Khaled Khari, ya ba da rahoto game da tabarbarewar al’amura a Gaza bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni da aka kwashe kusan watanni biyu ana aiki da ita.
“A kowace rana, muna kara nisa daga manufar mayar da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su zuwa gidajensu lami lafiya,” in ji Khari, yayin da yake magana kan fursunonin Isra’ila da aka yi garkuwa da su a Gaza.
Babban jami’in kula da harkokin siyasa na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a dawo da tattaunawar tsagaita bude wuta da kuma kai kayan agaji a Gaza ba tare da wata tangarda ba.
Ya yi ishara da jawabin da babban jami’in agaji na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher ya yi wa UNSC a farkon wannan makon, inda yace yin aiki da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ita ce hanya mafi dacewa domin kare fararen hula a Gaza, da kuma sako wadanda aka yi garkuwa da su, gami da shigar da kayan agaji da kayayyakin bukatar rayuwa zuwa Gaza.
Khari ya ce jami’an MDD shida na daga cikin daruruwan mutanen da aka kashe tun bayan da Isra’ila ta sake dawo da kai hare-hare a ranar Talata.
A daya bangaren kuma Majalisar Tarayyar Turai ta yi Allah wadai da “rugujewar yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwa da jikkatar fararen hula masu yawa a hare-haren jiragen saman Isra’ila a baya-bayan nan”.