Jam’iyyar “Turkish National Party” Ta Tsaid Imam Uglu A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa
Published: 24th, March 2025 GMT
Jami’iyyar adawa ta “Turkish National Party” ta bayyana cewa dan takararta a zaben shugaban kasa na 2028 shi ne magajin garin Istanbul Akram Imam Ugulu wanda a halin yanzu yake a gidan kurkuku.
Imam Uglu dan shekara 53 shi ne muhimmin dan takarar shugaban kasa a tsakanin ‘yan hamayya da ake hasashen cewa zai iya bugawa da shugaba Rajab Tayyib Urdugan a zabe mai zuwa.
‘Yan jam’iyyar ta adawa sun kada kuri’ar tsayar da Imam Ugulu a matsayin dan takararsu a zabe mai zuwa, inda ya sami kuri’u miliyan 1.6 a tsakanin miliyan 1.7.
Shugaban jam’iyyar ta “National Party” Uzgur Uzil wanda ya sanar da hakan, ya kuma bayyana cewa an yi zabe na gwaji da miliyoyin mutane su ka zabi Imam a matsayin shugaban kasa.
Kasar Turkiya ta fada cikin dambaruwar siyasa ne bayan da aka kama ‘yan hamayyar siyasa kusan 100 da aka zarga da cin hanci da rashawa, da kuma taimakawa ta’addanci. Daga cikin wadanda aka kama da akwai Akram Imam Uglu wanda shi ne magajin garin Istanbul.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Karfafa Gwiwar Kamfanonin Kasashen Duniya Da Su Fadada Zuba Jari A Sin
Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng ya bayyana a jiya Lahadi cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, kuma tana maraba da kamfanonin kasashen duniya da su fadada zuba jari a kasar Sin, domin zurfafa samun moriyar juna da samun nasara tare.
He ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin manyan kamfanoni na duniya a nan birnin Beijing, yayin da suka yi musayar ra’ayi kan yanayin tattalin arzikin duniya da na kasar Sin, da hadin gwiwar Sin da Amurka a fannin tattalin arziki da cinikayya, da fadada zuba jari a kasar Sin.
He ya ce, tattalin arzikin kasar Sin yana da karfin juriya, da fa’ida mai yawa, da wadataccen kuzari, ya kara da cewa, kasar Sin ta kuduri aniyar samun ci gaba mai inganci, da fadada bude kofa ga kasashen waje a babban mataki, da ci gaba da kyautata yanayin kasuwanci, tare da maraba da kara zuba jari da kamfanonin kasa da kasa suke yi a kasar Sin, don cin gajiyar damammakin da ke tattare da ci gaban kasar.
Shugabannin harkokin kasuwanci na kamfanoni na kasa da kasa da suka halarci wannan taro sun bayyana cewa, suna dora muhimmanci kan kasuwar kasar Sin, kuma suna da kwarin gwiwa game da makomar tattalin arzikin kasar Sin, kana sun bayyana aniyarsu ta yin hadin gwiwa na dogon lokaci tare da kasar Sin. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp