HausaTv:
2025-03-25@21:07:05 GMT

 Syria: Isra’ila Ta Kai Hari A Kan Sansanin Soja A Yankin Dar’a

Published: 24th, March 2025 GMT

Sojojin HKI sun kai wasu hare-hare akan sansanin sojan Sanamain dake gundumar Dara’a a kudancin kasar Syria.

Tashar talabijin din da “ Akhbariyyah” ta Syria ta sanar a yau Litinin cewa; sojojin Isra’ila sun kai hari akan sansanin soja na “Sanamain” wanda yake a gundumar Dar’a, kuma an ga jiragen sama na ‘yan mamaya masu yawa suna shawagi a samaniyar yankin.

Wata majiyar ta Syria ta kuma ambaci cewa; sojojin na HKI sun kursa cikin garin Mu’arrah, tare da  yin kutse cikin gidaje masu yawa a ciki da gudanar da bincike a cikinsu.

A yankin Kunaidhara ma an ga sojojin na mamaya suna yin kutse, haka nan kuma sun kai hari akan filin saukar jiragen sama na Tpor, da kuma wani filin saukar jiragen sama na soja a Tadammur.

Tun bayan da gwamnatin Basshar Assad ta fadi ne dai HKI ta bude kai wa makamai da cibiyoyin sojan kasar hare-hare babu kakkautawa. A cikin kwanakin farko na faduwar gwamnatin Asad, sojojin HKI sun sanar da cewa sun rusa tsakanin kaso 70% zuwa 80% na jumillar makaman da Syria take da su, na sama, kasa da na ruwa.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

UNRWA : hana shigar da kayan agaji Gaza, ya jefa yankin cikin matsanancin hali

Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ya yi gargadin cewa hana shigar da kayayyakin jin kai da Isra’ila ta yi a zirin Gaza ya jefa yankin cikin mawuyacin hali na rashin abinci.

“Makonni uku kenan da hukumomin Isra’ila suka hana shigar da kayayyaki cikin Gaza.

“Ba abinci, ba magani, ba ruwa, babu man fetur,” inji Philippe Lazzarini a cikin wani sako a shafukan sada zumunta.

Tun a ranar 4 ga watan Maris ne Isra’ila ta hana shigar da kayan agaji zuwa Gaza, bayan karewar kashi na farko na tsagaita bude wuta a yarjejeniyar da ta cimma da kungiyar gwagwarmayar falasdianwa ta Hamas data kunshi musayar fursunoni tsakanin bangarorin.

Lazzarini ya jaddada cewa al’ummar Gaza sun dogara ne kan shigo da kayayyaki daga yankunan da aka mamaye.

“Duk ranar da ta wuce ba tare da agajin jin kai ba, hakan na nufin yara da yawa suna kwana da yunwa, cututtuka na yaduwa,” in ji babban jami’in UNRWA.

Lazzarini ya bayyana haramcin taimakon a matsayin wani hukuncin bai daya ga al’ummar Gaza, wadanda akasarinsu kananan yara ne da mata.

Ya yi kira da a dage wannan kawanya da kuma kai agajin jin kai da kayayyakin kasuwanci zuwa Gaza.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan ta’adda Sun Kai Hari Sansanin Sojoji, Sun Kashe Uku A Borno
  • Za mu ɗauko hayar sojojin ƙetare domin horas da dakarun Nijeriya — Badaru
  • Dakarun Yemen sun kara kai hare-hare goyan bayan Falasdinu
  • UNRWA : hana shigar da kayan agaji Gaza, ya jefa yankin cikin matsanancin hali
  •  Arakci: Babu Wanda Zai Yi Tunanin Kawo Wa Iran Hari
  • Iran ta yi gargadin cewa keta hurumin Lebanon da Isra’ila ke yi barazana ne ga zaman lafiyar duniya
  • Duniya na ci gaba da yin tir da Isra’ila kan dawo da hare-harenta a Gaza
  • Isra’ila ta kashe wani mamba na ofishin siyasa na Hamas
  • Amurka ta sake kai hare-hare Yemen