‘Yansanda Sun Cafke Mutum 2 Kan Zargin Kashe Ɗan Achaɓa Da Sace Babur Ɗinsa A Bauchi
Published: 25th, March 2025 GMT
“Lokacin da aka samu rahoton faruwar lamarin, jami’an ‘yansanda ƙarƙashin jagoranci babban baturen ɗansanda (DPO) sun ziyarci wurin inda suka ɗauki gawar zuwa babban asibitin Darazo, a nan ne likita ya tabbatar da mutuwarsa,” Wakil ya shaida.
Yayin da bincike ya ci gaba da gudana, a ranar 20 ga watan Maris, ‘yansanda suka kama Yau Buba, ɗan shekara 25 mazaunin ƙauyen Minchika da ke Darazo a jihar Gombe tare da Mashin ɗin da aka sace daga hannun ɗan Achaɓan da aka kashe.
Wakil ya ƙara da cewa, a yayin da ake masa tambayoyi, shi Yau Buba ya bayyana da kansa cewa ya sayi Babur ɗin ne a hannun wani mutum mai shekaru 22 a duniya wato Buba Muhammadu, da suke ƙauye ɗaya a kan kuɗi Naira dubu ɗari biyu da hamsin ₦250,000.
Muhammadu shi ma an kamashi a ranar 21 ga watan Maris.
A halin da ake ciki an mayar da kes ɗin zuwa sashin kula da manyan laifuka (SCID) domin zurfafa bincike, “Idan aka kammala bincike kuma za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu,” PPRO ya tabbatar.
Har-ila-yau, rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta sake jaddada aniyarta na dakile ayyukan ta’addanci da wanzar da zaman lafiya da kare rayukan da dukiyar jama’a a fadin jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ɗansanda Ya Kashe Matar Abokin Aikinsa, Ya Jikata Wasu Biyu A Ribas
Wani Sufeto Dansandan da ke aiki a Jihar Kuros Ribas, ya harbe matar abokin aikinsa har lahira tare da jikkata wasu mutane biyu a harbe-harben da ya yi a ranar Lahadi.
Mai magana da yawun rundunar, SP Irene Ugbo, ta tabbatar da faruwar lamarin ga Labarai a birnin Kalaba, inda ta bayyana cewa jami’an Dansandan ya nuna halayyar da ba ta dace ba kafin ya fara harbe-harben.
Ba Na Goyon Bayan Dakatar Da Gwamnan Jihar Ribas – Ndume Bututun Iskar Gas Ya Sake Fashewa A RibasUgbo, ta ƙara da cewa jami’in, naaiki ne a Cibiyar ‘Yansanda ta Atakpa, ya dawo daga aikin dare a wani bankin ‘Microfinance’ kafin afkuwar lamarin. Ta kuma bayyana cewa tuni an kama wanda ake zargi, inda su kuma waɗanda suka jikkata ke samun kulawar likitoci a asibiti.
Bincike ya nuna cewa ɗansandan ya fara nuna alamun taɓun hankali tun bayan dawowarsa daga aikin dare, inda ya rufe ƙofar shiga ofishin ‘yansandan tare da hana kowa fita ko shigowa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp