Sin Ta Sanar Da Dokar Dakile Takunkuman Kasashen Waje
Published: 25th, March 2025 GMT
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya sanya hannu kan dokar majalisar gudanarwar kasar Sin, mai kunshe da matakan dakile takunkuman kasashen waje ta janhuriyar jama’ar kasar Sin.
Tanadin dokar zai fara aiki ne tun daga ranar kaddamar da ita. Dokar ta tanadi matakai da aka inganta na dakile takunkumai daga kasashen waje, da tsararrun matakan mayar da martani, da karfafa tsarin gudanar da ayyuka masu nasaba, tsakanin ofisoshin sassan majalisar gudanarwar kasar Sin, da karfafa matakan aiwatar da sassan dokar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa na fatan nasara ga tattaunawar Amurka da Iran
Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa na fatan nasara ga tattaunawar Iran da kuma Amurka.
Kasar Iraki ta bayyana fatan tattaunawar za ta aifar da kwanciyar hankali a yankin
Ministan harkokin wajen Iraki ya bayyana goyon bayansa ga tattaunawar tsakanin Iran da Amurka, yana mai bayyana fatan Bagadaza na ganin cewa hakan zai samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iraki ta fitar ta ce “Hussein ya karbi bakuncin mataimakin ministan harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh a ranar Juma’a a gidansa da ke birnin Antalya na Turkiyya.
Sanarwar ta kara da cewa “a yayin ganawar, an tattauna dangantakar da ke tsakanin kasashen dake makobtaka da juna da kuma hanyoyin karfafa su a fannoni daban-daban.”
“Hussein ya yi maraba da tattaunawar ta tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Amurka, yana mai bayyana fatansa na cewa a wannan shawarwarin za a samu sakamako mai kyau da zai taimaka wajen samun kwanciyar hankali a yankin.”
Shi ma babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA Rafael Grossi ya bayyana fatansa na ganin an cimma yarjejeniyar nukiliyar tsakanin Iran da Amurka cikin gaggawa.
Grossi ya ce yana da kwarin gwiwar cewa bangarorin biyu za su iya warware sabanin ra’ayi a fannin tattalin arziki da cinikayya ta hanyar yin shawarwari kafada-da-kafada da hadin gwiwa don cin moriyar juna.
Stephane Dujarric, mai magana da yawun babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana fatansa game da tattaunawar ta tsakanin Amurka da kuma Iran.