Aminiya:
2025-04-15@07:51:36 GMT

NAJERIYA A YAU: Yadda Ake Yi Wa ‘Yan Majalisar Ƙasa Kiranye

Published: 25th, March 2025 GMT

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Mulkin dimokuraɗiyya kamar yadda Hausawa ke cewa ‘yancin ɗan adam.

A lokacin da ta ba ka damar tsayawa don a zaɓe ka kan wani muƙamin, kazalika ta ba ka damar zaɓen wanda kake so ya shugabance ka kuma ya wakilce ka.

Wani abun da dimokuraɗiyyar ta bai wa al’umma dama a kai kuma shi ne na yin kiranye ga wakilan da suka zaɓa musamman idan waɗannan wakilan basa biya musu buƙatun da suka tura su a kai.

Tuni dai al’ummar Kogi ta Tsakiya suka fara kaɗa ƙuri’un kiranye ga Sanata Natasha da suka aike ga Majalisar Dattawa bisa dalilai nasu na ƙashin kan su.

NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a harkokin kasuwanci DAGA LARABA: Abin da doka ta ce kan dakatar da zaɓaɓɓen Gwamna

Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai tattauna ne kan matakai da sharuɗan da ake cikawa don yin kiranye ga ‘yan majalisa.

Domin sauke shirin, latsa nan

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Majalisar dattawa kiranye

এছাড়াও পড়ুন:

Abincin karnuka ya fi namu —Fursunonin Najeriya

Fursunoni a gidajen yarin daban-daban a sassan Najeriya sun koka game da munin irin abincin da ake ba su, wanda suka ce na karnuka ya fi shi.

Da dama daga cikin fursunonin da muka zanta da su sun bayyana cewa takwarorinsu sun sha mutuwa a sakamakon yunwa.

Wannan zargi na zuwa ne bayan da Hukumar Gidajen Yari ta Najeriya tare da wani kwamitin bincike mai zaman kansa sun ƙaryata zarge-zargen fursunonin kan yunwa a gidajen yari.

A watan Satumban 2024 ne Ministan Harkokin Cikin Gida,  Olubunmi Tunji-Ojo, ya kafa a kwamitin domin gudanar da bincike kan zargin jami’an gidajen yari da cin hanci da kuma cin zarafin fursunonin.

NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar Borno An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar Edo NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar Borno

Duk da cewa kwamitin ya tabbatar da zargin yunwa da fursunonin suka yi, Muƙaddashin Shugaban Hukumar Gidajen Yari ta Kasa, ya ce an zuzuta lamarin, saboda a cewarsa, babu alƙaluman da ke tabbatar da hakan.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Kashe Mutane Da Dama A Tsakiyar Najeriya
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Rikice-Rikice A Jihar Filato
  • Tsangayar Ilimi Ta BUK Ta Yi Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafuwa
  • Abincin karnuka ya fi namu —Fursunonin Najeriya
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar Borno
  • A daina cutar ’yan Najeriya ta hanyar rabon kayan tallafi
  • ’Yan adawa sun zama kyanwar Lami duk da rinjayensu a Majalisa
  • Tsohon kocin Super Eagles Christian Chukwu ya rasu
  • Yadda Ake Tuwan Amala Da Miyar Uwaidu
  • Yadda bom ya tashi da ɗan gwangwan a Legas