Dakarun Yemen sun kara kai hare-hare goyan bayan Falasdinu
Published: 25th, March 2025 GMT
Dakarun sojin Yaman sun ce sun kara kai hare-hare na nuna kyama ga Isra’ila da Amurka a matsayin nuna goyan baya a kan zirin Gaza.
Kakakin rundunar Yahya Saree ya ce a daren jiya litinin sojojin na Yaman sun kai hari filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion na Isra’ila da makami mai linzami guda biyu da suka hada da Zulfiqar mai gudun tsiya.
Ya kara da cewa hare-haren na goyon bayan Falasdinawa ne a Gaza.
Saree ya yi nuni da cewa, dakarun kasar Yemen sun kuma kai hari kan jirgin yakin Amurka Harry S.
Saree ya ce harin da aka kai kan jiragen ruwan yakin Amurka shi ne irinsa na biyu cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Ya ce an kai harin ne domin mayar da martani ga hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar ta Yemen.
Saree ya kuma jaddada cewa za a ci gaba da gudanar da ayyukan adawa da Isra’ila har sai an daina ta’addancin gwamnatin tare da dage killacewar da aka yi wa Gaza.
A ranar 15 ga Maris, Amurka ta sanar da kai wani hari ta sama da ya yi sanadin mutuwar ‘yan kasar Yemen 53.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas : Isra’ila ta yi amfani da sulhu wajen tattara bayanai kan shugabannin Hamas domin kashe su
Kungiyar gwagwarmayar falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa Isra’ila ta yi amfani da sulhun da aka cimma wajen tattara bayanai kan shugabannin kungiyar ta bi tana kashe su.
Saidai mai magana da yawun kungiyar ya ce kungiyar tana da tushe sosai a Falasdinu wanda kisan gillar da Isra’ila ke yi wa shugabanninta ba, bai zai rusa ta ba.
Sami Abu Zuhri ya bayyana hakan ne bayan da Isra’ila ta kashe wasu jami’an ofishin siyasa na kungiyar ta Hamas guda hudu cikin kasa da mako guda tun bayan da ta koma yakin kisan kare dangi a zirin Gaza, wanda hakan ya saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta na tsawon watanni biyu da Hamas.
Jinin shugabanni da kwamandojin Hamas iri daya ne da na yara da matasa na Gaza, kuma wadannan kashe-kashen ba za su hana mu ci gaba da gwagwarmaya ba.
Kakakin na Hamas ya kuma nuna rashin jin dadin yadda Isra’ila ke aiwatar da hukuncin kisa a kullum a yankin da aka yi wa kawanya.
“Abin da ke faruwa a Gaza a yanzu ya fi yakin kisan kare dangi da aka shafe watanni 15 ana yi,” in ji shi.
Rahotanni na baya-bayan nan na cewa, akalla Falasdinawa 23 da suka hada da kananan yara bakwai ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai da kafin wayewar gari a wannan Talata.