Ministan Lafiya Ya Yi Alƙawarin Inganta Tallafi Ga Likitoci A Hajjin 2025
Published: 25th, March 2025 GMT
“Duba da yanayin kiwon lafiya a duniya tun bayan ɓullar cututtuka kamar sanƙarau da Shan Inna, wajibi ne mu bi ƙa’idojin kiwon lafiya na Saudiyya.
“Dole ne mu tabbatar da cewa dukkanin alhazai sun samu takardun rigakafi da katin shaidar lafiya,” in ji shi.
Ministan, tare da rakiyar wasu manyan jami’an ma’aikatar lafiya, sun duba motocin ɗaukar marasa lafiya na NAHCON, kayan magani, da shirye-shiryen kiwon lafiya a asibitocin Nijeriya da ke Saudiyya.
Sun gano muhimman wuraren da ake buƙatar ingantawa, ciki har da wadatar magunguna, alluran rigakafi, na’urorin likitanci, da motocin ɗaukar marasa lafiya.
Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya yaba da shirin Ministan, inda ya ce: “Ziyararku ta ƙara mana ƙwarin gwiwa a ƙoƙarin da muke yi na inganta kiwon lafiyar alhazai.”
A duk shekara, kimanin ‘yan Nijeriya 70,000 ne ke halartar aikin Hajji, kuma Ministan Pate ya bayyana damuwarsa kan matsalolin da ke tattare da yanayin zafi mai tsanani da ake tsammanin fuskanta a Hajjin 2025.
Ya ce an ɗauki matakan kariya don tabbatar da lafiyar alhazai da jin daɗinsu.
Wannan shiri na haɗin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Lafiya da NAHCON zai tabbatar da cewa mahajjatan Nijeriya sun samu ingantacciyar kulawa.
NAHCON ta kuma tabbatar da ƙudirinta na ci gaba da samar da ingantattun ayyuka ga alhazai.
Waɗanda suka halarci wannan ziyarar sun haɗa da Minista Pate, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, Kwamishinan Ayyuka Prince Anofi’u Olanrewaju Elegusi, Farfesa Abubakar Abubakar Yagawal, Prince Abdul-Razak Aliyu, Dokta Sa’edu Ahmad Dumbulwa da sauran manyan jami’ai na NAHCON da Ma’aikatar Lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Alƙawari Kiwon Lafiya kiwon lafiya tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Ce Zargin Kasar Amurkan Dangane Da Kamfanonin Man Fetur Na Kasar Ba Gaskiya Bane
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya musanta zargin kasar Amurka na cewa wasu jiragen ruwan JMI suna amfani da tudan kasar Iraqi sun kai kawo a ruwayen yankin.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fadawa Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran, kan cewa Aragchi yana fadar haka ne a jiya litinin, a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Iraki Fu’ad Hussain.
Kafin haka ministan ya nakalto korafin da jami’an gwamnatin kasar Amurka suka gabatarwa gwamnatin kasar Iraki na cewa jiragen ruwan kasar Iran na amfani da takardun bugi na kasar Iraki don gudanar da harkokinsu a yankin. Aragchi ya musanta hakan ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Amurka tana son raba JMI da dukkan kasashe makobta don cimma manufofinta na maida kasar Iran saniyar ware a duniya.
Ministocin biyu sun tattauna batun abubuwan da suke faruwa a yankin Asiya ta kudu wadanda suka hada da bautun kissan kiyashin da yahudawan sahyoniyya suke yi a kasar Falasdinu da aka mamaye.
A nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Iraqi ya ce kasar Iraki bada cikin kwancen masu gwagwarmaya a yankin. Wannan kamar yadda kowa ya sani bukata ce daga kasar Amurka na gwamnatin kasar Iraki ta fidda kanta daga kawancen gwagwarmaya wanda kasar Iran take jagoranta a yankin.