Lauyoyi 77 a Jamus sun yi kira ga gwamnati da ta mutunta sammacin ICC na cafke Netanyahu
Published: 25th, March 2025 GMT
Wasu lauyoyi 77 a Jamus sun bukaci gwamnatin kasar da ta mutunta sammacin kotun hukunta manya laifuka ta duniya ICC, na cafke firaministan Isra’ila Banjamin Netanyahu.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da da suka fitar, fitattun lauyoyin 77 sun kuma bayyana yiwuwar kasancewar Netanyahu a Jamus a matsayin take doka da kuma hakkin kasar.
Lauyoyin sun soki Friedrich Martin Josef Merz, dan siyasa kuma shugaban gwamnati a nan gaba, saboda sanarwar da ya yi a lokacin yakin neman zabe cewa zai samo hanyar gayyatar firaministan Isra’ila da kuma tattaunawa ta wayar tarho da Netanyahu bayan nasararsa.
Lauyoyin sun kuma yi Allah wadai da halin wasu jami’o’in da suka soke jawabin da Francesca Albanese mai kula da harkokin kare hakkin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi a yankin Falasdinu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
EFCC Ta Cafke Mutum 21 Bisa Zarginsu Da Zambar Intanet A Bauchi
Jami’an Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) na shiyyar Gombe, sun kama wasu mutane 21 da ake zargi da damfarar Intanet a Jihar Bauchi.
A cewar wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Litinin, “An kama wadanda ake zargin ne ta hanyar samun sahihan bayanan sirri kan zargin da ake yi musu na damfarar Intanet a yankin Kaure New Government Reservation Area, Bauchi da Awala, a titin Maiduguri, Jihar Bauchi.
Gwamnatin Tarayya Ta Karbi Rukunin Farko Na Taraktoci Dubu Biyu Daga Belarus Matasa 4 Sun Yi Garkuwa Da Yaro, Sun Kashe Shi A Bauchi“Abubuwan da aka kwato daga hannunsu a wajen kama su sun hada da motoci kirar BMW daya da Toyota Camry, PlayStation 5 guda uku, wayoyi masu tsada 30, da babbar talabijin daya, injin PoS guda shida, iPad guda hudu, da kwamfyutoci biyar.”
Sanarwar ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp