HausaTv:
2025-03-25@21:14:36 GMT

Rasha ta ce tana nazari kan sakamakon tattaunawar

Published: 25th, March 2025 GMT

Kasar Rasha ta bayyana a wannan Talata cewa tana nazarin sakamakon tattaunawar da ta yi da Amurka kan Ukraine a Saudiyya,

Rasha ta ce ba wani bayyani da za’a fitar game da tattaunawar, kuma ba wani lokaci da aka a sanya na ranar da za a sake ganawa da Amurkawa ba.

“An ba da sakamakon tattaunawar da aka yi a manyan biranen, Kuma “Ana nazarin su,” in ji mai magana da yawun shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov yayin jawabinsa na yau da kullun.

Rahotanni sun ce ana tattaunawa tsakanin Amurka da Ukraine har zuwa yau Talata.

Bayan shafe sa’o’i 12 na tattaunawar sirri da aka yi a Saudiyya, jami’an Amurka da na Rasha sun kammala tattaunawa kan rikicin Ukraine a ranar Litinin.

Hukumomin Rasha sun ruwaito cewa fadar White House da Kremlin za su fitar da sanarwar hadin gwiwa yau Talata kan tattaunawar da suka yi, wanda Moscow ta bayyana tun da farko a matsayin “mai wuyar gaske.”

Tattaunawar yanzu tana mai da hankali kan yiwuwar tsagaita wuta a tekun Black Sea, domin ba da damar komawa kan yarjejeniyar da ta bai wa Ukraine damar fitar da hatsin da yake da muhimmanci ga samar da abinci a duniya.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

 Shugaban Majalisar Dokokin Lebanon Ya Yi Gargadi Akan Masu Tunanin Kulla Alakar Kasar Da HKI

Shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Barri ya jaddada cewa; HKI tana kokarin jefa Lebanon cikin tarkon kulla alaka da ita, yana mai jaddada cewa; Ko kadan Lebanon ba ta kama wannan hanyar ba.

Nabih Barri ya bayyana yadda wasu rahotanni daban-daban suke Magana akan cewa Amurka tana kai gwauro da mari, domin ganin an bude alaka kai tsaye a tsakanin Lebanon da HKI.

Shugaban majalisar dokokin kasar ta Lebanon ya ce, ko kadan kasar Lebanon ba ta tunanin kulla alaka da HKI.

Haka nan kuma ya yi ishara da tsagaita wutar yaki wacce a kodayaushe HKI take ketawa, yana mai tabbatar da cewa Hizbullah tana riko da ita, don haka ya yi kira ga Amurka da sauran bangarorin da suke a cikin tsagaita wutar da su yi matsin lamba ga HKI domin ta yi aiki da ita.

Bugu da kari Nabih Barri ya ce; Sojojin kasar ta Lebanon sun gama shiryawa domin shiga cikin kudancin tafkin Laitani, amma matsalar da ake fuskanta ita ce yadda Isra’ila take kin janyewa daga wasu yankuna a cikin Lebanon.

Nabih Barri ya kuma jaddada cewa; Kungiyar Hizbullah tana aiki da tsagaita wutar yakin, kuma ba ta keta ta ba ko kadan.

Shugaban Majalisar Dokokin kasar ta Lebanon ya kara da cewa; Duk da cewa HKI tana keta tsagaita wutar yaki, amma ko sau daya Hizbullah ba ta harba ko harsashi daya ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ukraine: Tawagogin Rasha da Amurka sun kammala tattaunawa a Saudiyya
  • Kiyaye Ci Gaba Mai Dorewa A Huldar Sin Da Amurka Ya Dace Da Moriyar Sasssan Biyu
  • An Yi Taron Tattaunawar Kasa Da Kasa Kan Damammakin Da Sin Ke Gabatarwa A Rasha
  •  Shugaban Majalisar Dokokin Lebanon Ya Yi Gargadi Akan Masu Tunanin Kulla Alakar Kasar Da HKI
  • Gobara ta tashi a gidan mai sakamakon fashewar tanka a Neja
  • Za’a Gudanar Taron Tattaunawa Tsakanin Rasha Ta Amurka A Karo Na Biyu 2 A Birnin Rayad na Kasar Saudiya
  • Moscow : Dole ne Rasha da China su shiga tattaunawar nukiliya da Iran
  • Ɗan sa-kai ya kashe matasa biyu a Borno
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [15]