Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya musanta zargin kasar Amurka na cewa wasu jiragen ruwan JMI suna amfani da tudan kasar Iraqi sun kai kawo a ruwayen yankin.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fadawa Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran, kan cewa Aragchi yana fadar haka ne a jiya litinin, a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Iraki Fu’ad Hussain.

 Kafin haka ministan ya nakalto korafin da jami’an gwamnatin kasar Amurka suka gabatarwa gwamnatin kasar Iraki na cewa jiragen ruwan kasar Iran na amfani da takardun bugi na kasar Iraki don gudanar da harkokinsu a yankin. Aragchi ya musanta hakan ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Amurka tana son raba JMI da dukkan kasashe makobta don cimma manufofinta na maida kasar Iran saniyar ware a duniya.

Ministocin biyu sun tattauna batun abubuwan da suke faruwa a yankin Asiya ta kudu wadanda suka hada da bautun kissan kiyashin da yahudawan sahyoniyya suke yi a kasar Falasdinu da aka mamaye.

A nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Iraqi ya ce kasar Iraki bada cikin kwancen masu gwagwarmaya a yankin.  Wannan kamar yadda kowa ya sani bukata ce daga kasar Amurka na gwamnatin kasar Iraki ta fidda kanta daga kawancen gwagwarmaya wanda kasar Iran take jagoranta a yankin.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: gwamnatin kasar kasar Amurka kasar Iraki

এছাড়াও পড়ুন:

Al-Huthi Ya Ce Kawo Wani Jirgin Ruwa Mai Daukar Jiragen Saman Yaki Gazawa Ce Ga Amurka

Shugqbqn kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen sayyed Abdulmalik Badaruddin Huthi ya bayyana cewa tura wani kataparen jirgin ruwan yaki zuwa gabas ta tsakiya wanda shugaban kasar Amurka yayi wata gazawace.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalti Alhuthi yana fadar haka yau Lahadi a wani jawabin da ya gabatar ,inda yake bayyana irin halin da ake ciki a yakin da sojojin kasarsa suke fafatawa da gwamnatin kasar Amurka.  Ya kuma kara da cewa jiragen yakin ruwa na kasar Amurka sun zama matsala ga gwamnatin Amurka maimakon su taimaka mata.

Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan cewa zata aiko da jirgin ruwan yaki mai suna USS Carl Vession zuwa tekun Maliya don karfafa USS Harry Truman a yakin da take fafatawa da sojojin kasar Yemen.

Shugaban kungiyar Ansarullah ya bayyana cewa sojojin kasar Yemen zasu ci gaba da abinda suka sa a gaba na maida martini kan jiragen yakin Amurka a tekun Red Sea da kuma dukkan jiragen HKI ko wadanda suke zuwa can don tallafawa mutanen Gaza.

Shugaban kasar Amurka donal Trump dai ya sha alwashin shefe kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen daga Doron kasa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Alamar Deepseek” Ta Bude Kofar Gyara Na Kara Kunno Kai A Harkokin Duniya
  • Iran Ta Turkiyya Sun Bukaci kasashen Musulmi Su Magance matsalar Jinkai A Kasar Palasdinu Da Aka Mamaye
  • Za mu ɗauko hayar sojojin ƙetare domin horas da dakarun Nijeriya — Badaru
  • An Yi Taron Tattaunawar Kasa Da Kasa Kan Damammakin Da Sin Ke Gabatarwa A Rasha
  •  Arakci: Babu Wanda Zai Yi Tunanin Kawo Wa Iran Hari
  • Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Karfafa Gwiwar Kamfanonin Kasashen Duniya Da Su Fadada Zuba Jari A Sin 
  • Al-Huthi Ya Ce Kawo Wani Jirgin Ruwa Mai Daukar Jiragen Saman Yaki Gazawa Ce Ga Amurka
  • Gwamnatin Kano Ga Ma’aikata: Duk Mai Bukatar Aikinsa Dole Ya Gabatar Da Kansa A Wajen Tantancewa
  • Amurka ta cire tukuicin wanda ya bayar da bayani kan mataimakin shugaban Taliban