Dalilin da dimokuraɗiyya ta gaza kawo ci gaba a Afirka — Obasanjo
Published: 25th, March 2025 GMT
Tsohon Shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ce mulkin dimokuraɗiyya ya gaza wajen kawo ci gaba a nahiyar Afirka.
Ya ce tsarin ya gaza ne saboda abin da ya ƙunsa bai zo daidai da al’adu, da yadda ake tafiyar da rayuwa a nahiyar ba, da abubuwan da mutanen nahiyar suka yi amanna da su ba.
Gidauniyar Zakkah ta raba wa marayu 100 kayan sallah a Gombe Kantoman Ribas ya naɗa sabon Sakataren GwamnatiTsohon shugaban na wannan furuci ne a Abuja a wurin wani taron bikin cika shekaru 60 a duniya na tsohon mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai kuma tsohon Gwamnan Imo, Emeka Ihedioha.
Obasanjo ya buga misali da yadda tsohon shugaban Amurka, Abraham Lincoln, ya bayyana tsarin dimokuraɗiyya da cewa gwamnati ce ta mutane da mutane ke jagoranta domin al’umma.
Ya ƙara da cewa tsari ne da ake yu domin kowa ya amfana, ba wai wani ɓangaren na al’umma ba ko wasu mutane ƙalilan ba.
Obasanjo ya kuma bayyana cewa kafin zuwan dimokuraɗiyyar ƙasashen yamma, Afirka na da nata tsarin shugabancin wanda ke kula da buƙatun kowa.
A cewarsa wannan tsarin shi ne dimokuraɗiyya, ba abin da ake kira dimokuraɗiyya ba a yau wanda ke bai wa shugabanni damar karɓar duk abin da suke so ba bisa ƙa’ida ba da kuma ta hanyar cin hanci da rashawa su ce wa mutane su je kotu idan suna da ja.
Obasanjo ya ce matuƙar ba a sake fasalin dimokuraɗiyya ta yi daidai da al’adu da manufofin ’yan Afirka da kuma mutunta buƙatun jama’a ba, to za ta ci gaba da durƙushewa kuma a ƙarshe ta mutu murus a nahiyar.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da tsoffin gwamnonin Anambra da Ribas —Peter Obi da Rotimi Amaechi.
Sauran mahalartan sun haɗa da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, tsoffin Shugabannin Majalisar Dattawa — David Mark da Ken Nnamani da tsoffin gwamnonin Sakkwato da Kuros Riba — Aminu Waziri Tambuwal da Donald Duke.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dimokuraɗiyya Obasanjo ya
এছাড়াও পড়ুন:
Nijeriyar Jiya Da Yau: Kiki-Kakar Sabgar ‘Yan Majalisu
Ba wannan tarihi na kanfar iko da ayarin farko na “yan majalisun wannan kasa ke da shi ne abin kallo ko la’akari ba, cikakkiyar dama da suke da ita a yau, tare da turbude hancin bukatun masu zabe, shi ne babban abin nadama da kaico!!!. Idan a wancan lokaci za a ce Turawa sun rike musu kugu ne, ta yadda za a ga ba su da wani tasiri ko katabus, wajen zuwa da kyawawan manufofi, don ciyar da jama’arsu gaba. Yanzu kuwa, za a iya yi wa wadannan “yan majalisun uzuri?. Shin, suna da cikakken ikon gudanar da aiyukan nasu ko babu?. Babu shakka, duk wani irin iko da ake da bukata da tsarin mulki zai ba da, ya jima da bai wa “yan majalisun namu wannan iko ko dama a yau. To a ina ne yanzu gizo ke sakar? Cikin batutuwan da za a bijirar gaba, a nan ne kowa ke da ikon yin tsifa game da gurbacewar al’amuran majalisa a Nijeriyar yau.
“…The composition and functioning of the legislatibe council, howeber, pointed to the fact that, it was nothing more than a mere rubber-stamping institution…”.
(Fagge & Alabi, 2007: 5b).
Wadancan kalamai na sama cikin harshen Turanci, na yin nuni ne da cewa, “yan majalisun Nijeriya a wancan lokaci da Turawan Birtaniya ke mulkarmu, ba su kasance komai ba, face “yan-abi-yarima ne cikin harkokin zaman majalisar. Duk abinda aka yanke a majalisar, kawai sai dai su sanya-hannu ne akai. Ba su da ikon tabbatar da wani kudiri, koko yin watsi da shi. Tun da, hatta mafi yawan adadin mutanen da ke cikin zauren na majalisar, za a samu cewa, gwamna ne ya zabe su da hannunsa, kamar yadda a rubutun baya aka faiyace irin adadinsu dalla-dalla.
Batun rashin iko, ko karancinsa, shi ne babban abinda ya mamaye harkokin “yan majalisun na kasa gabanin Nijeriya ta kai ga samun “yancin-kai. Sai dai, a kan samu wasu “yan canje-canje ne daga lokaci zuwa lokaci, sakamakon mabanbantan kundin tsarin mulkin da Turawan suka gabatar mana da su gabanin kai wa ga samun yancin-kai. Tulin labaran “yan majalisun na da auki ainun, kawai za mu yi kokarin matsawa gaba ne cikin hanzari, don kai wa ga yadda lamuran majalisar ke wakana a yau, wanda shi ne babban abinda muke son yin doguwar tattaunawa akai sannu a hankali.
“Yan Majalisunmu A Shekarar 1900
Ya tabbata, bayan samun “yancin-kai a wannan Kasa (cikin Shekarar 19b0), “yan majalisun namu, sun kai ga fara samun “yancin gudanar da aiyukansu, sama da irin yadda suka kasance a baya. Tsarin mulki irin na shugaban kasa daban, da shugaban gwamnati (tsarin mulkin firaminista) daban, aka fara dabbakawa a wannan kasa bayan samun mulkin kai. A karkashin tsarin mulkin, za a ga irin aikace-aikacen da wadannan ‘yan majalisun namu na lokacin suka gudanar, kafin juyin mulkin Soja na farko da aka fara yi a kasar, cikin Shekarar 19bb, Shekaru shida (b) kacal, bayan samun yancin-kai. Ke nan, irin ayyukan da suka gudanar cikin majalisar, zai zamto ne a tsakanin Shekarar 1900 da Shekarar 1900.
Ga wasu daga irin ayyukan da bangaren “yan majalisun suka gudanar kamar haka;
i- Kafa Gwamnati: “yan majalisun ne suka taka rawa wajen zabar firaminista Abubakar Tafawa Balewa a matsayin shugaban gwamnati, tare da yunkurin fasalta tsarin gwamnatin dimukradiyya.
ii- Ci gaban bangaren dokoki: “yan majalisun, sun samar da dokoki kyawawa, musamman wadanda suka shafi ci gaban tattalin arzikin kasa, ilimi tare da samun cikakken ikon gudanarwa a cikin lardunan kasar da ake da su.
iii- Kyautata Wakilci A Gwamnatin Hadaka Da Na Larduna: tsarin, ya ba da dama ga jagororin gwamnati (firimiyoyi) na lardunan arewa da yamma da na gabashin kasar, na su shigo cikin lamuran gudanar gwamnati dumu-dumu, don a dama da su.
ib- Canjin Mirginawar Tsarin Mulki Na Kasa: “yan majalisun, sun taka rawa muhimmiya, wajen dawowar tsarin mulkin dake nuna lamuran Kasar, na gudana karkashin ikon Sarauniyar Birtaniya ne, zuwa ga wata jamhuriya mai zaman kanta cikin Shekarar 19b3, wadda ikonta ya sabbawa Dr Nnamdi Azikiwe zama shugaban kasar Nijeriya na farko.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp