Super Eagles ta gamu da cikas a ƙoƙarin neman tikitin Gasar Kofin Duniya
Published: 26th, March 2025 GMT
Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta gamu da cikas a ƙoƙarinta na neman yankar tikitin shiga Gasar Kofin Duniya ta baɗi, bayan da ta tashi canjaras 1-1 da Zimbabwe.
Victor Osimhen ne ya fara ci wa Nijeriya kwallo a minti na 74 a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom.
Sai dai Zimbabwe ta farke ana daf da tashi a minti na 90 ta hannun ɗan wasanta na gaba, Taranda Chirewa.
Wannan sakamako na nufin cewa Nijeriya na matsayi na huɗu a rukunin C, inda Ghana ke gabanta a matsayi na ɗaya da kusan ratar maki shida bayan buga wasanni shida.
Wasan da Nijeriya za ta yi Bafana Bafana a watan Satumba, zai kasance mai matuƙar muhimmanci, la’akari da cewa ƙasar da ke saman kowane rukuni ne kaɗai ke samun damar zuwa Gasar Kofin Duniya.
A ranar Juma’a ce tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta doke Rwanda da ci 2-0 a birnin Kigali a wasannin neman gurbin shiga Gasar Kofin Duniya.
Ɗan wasan Nijeriya Victor Osimhen ne ya zura duka ƙwallayen biyu gabanin hutun rabin lokaci.
A lokacin Nijeriya ta koma matsayi na huɗu a cikin ƙasashe shida da ke Rukunin C bayan wasanni biyar-biyar.
Ƙasar da ta zama ta farko a kowane rukuni daga cikin rukunai tara na ƙasashen Afirka ne ke da tabbacin shiga gasar kofin na duniya, wanda a karon farko aka faɗaɗa zuwa ƙasashe 48.
Sai kuma za a zaɓi ƙasashe huɗu da suka fi ƙoƙari daga cikin waɗanda suka zama na biyu, sai su fafata wasan kifa-ɗaya-ƙwala na neman cike gurbi, inda waɗanda suka samu nasara za su iya samun damar shiga gasar.
Sauran wasannin da suka rage wa Super Eagles su ne na ranar 1 ga Satumba wanda Nijeriya za ta yi da Rwanda sai na ranar 8 ga Satumba tsakaninta da Afirka ta Kudu da kuma na ranar 6 ga Oktoba da za ta fafata da Lesotho sai cikon na ƙarshe wanda za ta yi karon batta da Benin a ranar 13 ga Oktoba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gasar Kofin Duniya Nijeriya Kofin Duniya shiga Gasar Gasar Kofin
এছাড়াও পড়ুন:
Wasu manyan ’yan Nijeriya sun yi wa Gwamna Radda ta’aziyya a Saudiyya
Wasu manyan ’yan Nijeriya da suka tafi Umarah sun yi wa Gwamnan Katsina Dikko Umar Radda ta’aziyya a Saudiyya.
A safiyar Lahadi ce dai Allah Ya karɓi rayuwar mahaifiyar Gwamnan, Hajiya Safara’u Umaru Baribari bayan shafe tsawon lokaci tana jinya a Jihar Katsina.
Wata mata ta haifi jaririn da ba nata ba NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a harkokin kasuwanciBayan rasuwar ce gwamnoni da wasu fitattun ’yan siyasa da a halin yanzu suna ƙasa mai tsarki suka kai wa Gwamna Radda ziyara domin jajanta masa dangane da wannan babban rashi.
Daga cikin gwamnonin akwai Mohammed Umar Bago na Jihar Neja, da Farfesa Babagana Zulum na Jihar Borno da Gwamna Uba Sani na Kaduna, da Dauda Lawal Dare na Zamfara da kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe
Sauran fitattun ’yan siyasar da suka ziyarci Gwamna Radda sun haɗa da Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, da tsohon Gwamnan Bauchi, Ahmed Mu’azu.
Akwai kuma fitaccen attajirin nan kuma ɗan kasuwa, Alhaji Dahiru Mangal da kuma tauraron tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta Super Eagles, Ahmed Musa da su ma suka jajanta wa gwamnan a kan rashin.
Dukkansu sun bayyana alhini tare da roƙon Allah Ya jiƙan Hajiya Safara’u Ya sa ta huta.