‘Yan ta’adda Sun Kai Hari Sansanin Sojoji, Sun Kashe Uku A Borno
Published: 26th, March 2025 GMT
Hakan ya sa, rundunar FOB ta yi kira da akawo musu dauki ta sama baya ga aikewa da karin tawaga ta kasa domin tallafawa. Duk da haka, tawagar ta sake cin karo da Bam a kan hanya.
Duk da cewa, ba a samu cikakken bayanin harin ba a lokacin rubuta wannan rahoton, amma an samu cewa, matukin jirgin yakin da aka aika domin bayar da agaji ta sama, ya sanar da cewa, yana iya hango wuta tana ta shi a kusa da FOB sannan wasu sojoji da dama na gudu zuwa Sabon Gari, kamar dai, an riga an kwace sansanin FOB din.
Darakta, Ayyukan Yada Labarai na Tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, bai amsa sakon da Wakilinmu ya aika masa ba domin tabbatarwa a lokacin fitar da wannan rahoton.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi 34 na Katsina
A wannan Litinin ɗin ce ne aka rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi 34 na Jihar Katsina waɗanda aka gudanar da zaɓensu a ranar 15 ga watan Fabrairu, 2025.
Babban Jojin Jihar Katsina, Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar ne ya jagoranci rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomin.
’Yar shekara 66 ta haifi ɗanta na 10 da kanta Bello Turji ya kashe manoma 11 a SakkwatoSai dai gab da lokacin da za a rantsar da su, ɗaya daga cikinsu ya faɗi ya sume a lokacin da yake ƙoƙarin shiga rumfar da aka tanadar masu.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Bakori Honarabil Aminu Ɗan Hamidu shi ne wanda ya faɗi kuma aka ɗauka ranga-ranga zuwa asibiti.
Binciken da muka yi ya nuna cewa, shugaban ya take wani sashe na babbar rigar shi ne ba tare da ya yi la’akari ba yayin da ya yunƙura da ƙarfi don hawa matattakalar shiga rumfar, lamarin da ya janyo rigar ta shaƙe shi ya faɗi a sume.