Jarumin Kannywood Baba Ƙarƙuzu ya rasu
Published: 26th, March 2025 GMT
A yanzu nan ne Aminiya take samun labarin rasuwar fitaccen jarumin Kannywood, Malam Abdullahi Shu’aibu wanda aka fi sani da Baba Ƙarƙuzu ko Ƙarƙuzu na Bodara.
Hakan dai na kunshe ne cikin wani sako da jarumi a masana’antar Kannywood kuma Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Kano, Abba El-Mustapha, ya wallafa a shafinsa na Instagram.
SShi ma dai fitaccen jarumin Kannywood kuma Shugaban Hukumar Fina-finai ta Nijeriya, Ali Nuhu, ya wallafa hoton marigayi Ƙarƙuzu a shafinsa na Facebook yana mai roƙon Allah Ya jikansa.
Ƙarƙuzu dai tsohon jarumi ne a masana’antar Kannywood da ya yi tashe tun a shekarun 1980.
Ana iya tuna cewa wata hira da ya yi da Zinariya TV kuma Mujallar Fim ta wallafa a shekarar 2023, Ƙarƙuzu wanda ya nemi taimakon jama’a ya sanar da cewa ya makance kuma yana fama da matsananciyar rashin lafiya.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas : Isra’ila ta yi amfani da sulhu wajen tattara bayanai kan shugabannin Hamas domin kashe su
Kungiyar gwagwarmayar falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa Isra’ila ta yi amfani da sulhun da aka cimma wajen tattara bayanai kan shugabannin kungiyar ta bi tana kashe su.
Saidai mai magana da yawun kungiyar ya ce kungiyar tana da tushe sosai a Falasdinu wanda kisan gillar da Isra’ila ke yi wa shugabanninta ba, bai zai rusa ta ba.
Sami Abu Zuhri ya bayyana hakan ne bayan da Isra’ila ta kashe wasu jami’an ofishin siyasa na kungiyar ta Hamas guda hudu cikin kasa da mako guda tun bayan da ta koma yakin kisan kare dangi a zirin Gaza, wanda hakan ya saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta na tsawon watanni biyu da Hamas.
Jinin shugabanni da kwamandojin Hamas iri daya ne da na yara da matasa na Gaza, kuma wadannan kashe-kashen ba za su hana mu ci gaba da gwagwarmaya ba.
Kakakin na Hamas ya kuma nuna rashin jin dadin yadda Isra’ila ke aiwatar da hukuncin kisa a kullum a yankin da aka yi wa kawanya.
“Abin da ke faruwa a Gaza a yanzu ya fi yakin kisan kare dangi da aka shafe watanni 15 ana yi,” in ji shi.
Rahotanni na baya-bayan nan na cewa, akalla Falasdinawa 23 da suka hada da kananan yara bakwai ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai da kafin wayewar gari a wannan Talata.