Sudan: RSF ta hana kayan agaji a yankunan da ke a karkashin ikonta
Published: 26th, March 2025 GMT
Dakarun (RSF) sun sanya sabbin takunkumai kan isar da kayan agaji a yankunan da ke karkashin ikonsu, lamarin da ya kara ta’azzara matsalar ayyukan jin kai, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
Matsalolin dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar RSF ke kokarin kafa gwamnatin daga bangarenta a yammacin kasar ammacin Sudan, duk da fatattakarsu sojojin kasar suka yi daga babban birnin kasar, Khartoum, lamarin da ke barazana ga rarrabuwar kawuna a kasar da yaki ya daidaita.
Matakan da kungiyar ta dauka na hana gudanar da ayyukan agaji na barazana ga rayuwar dubban daruruwan mutane a yankin na Darfur, wadanda da dama daga cikinsu sun riga sun rasa matsugunansu sakamakon tashe-tashen hankula a baya.
A baya ma’aikatan agaji sun zargi mayakan RSF da wawushe kayan agaji a tsawon fiye da shekaru biyu da ake fama da tashin hankali a Sudan, lamarin da ke kara ta’azzara yunwa da cututtuka a kasar.
Ma’aikatan agaji goma sha biyu, da suka yi magana da kamfanin dillancin labarai na Reuters, sun ce tun a karshen shekarar da ta gabata, kungiyar ta RSF ta fara neman karin kudade da kuma sa ido kan yadda ake gudanar da ayyuka, kamar daukar ma’aikatan cikin gida da tsaro, da irin tsarin da hukumomin da ke da alaka da sojoji ke amfani da su, da kuma kara tsaurara hanyoyin shiga.
A baya dai ba a bayar da rahoton wannan yunkuri na RFS ba, amma kungiyoyin agaji na kasa da kasa sun fara ja da baya sakamakon matsanancin yanayin da ake ciki.
A cewar ma’aikatan agaji, yunƙurin da RSF ke yi ya kawo babban cikas ga ayyukansu, wanda ke nuni da yiwuwar fadawar miliyoyion mutane a cikin matsanancin hali na yunwa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Kashe Mutane Fiye Da 300 A Wani Kazamin Fada A Yankin Darfur Da Ke Yammacin Kasar Sudan
Mutane fiye 300 ne suka mutu a cikin kwanaki a wani kazamin fada a yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan
Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta watsa rahoton cewa: Sama da fararen hula 300 ne aka kashe a wani kazamin fada na kwanaki biyu a yankin Darfur na kasar Sudan mai fama da rikici.
Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun kaddamar da hare-hare a ranakun Juma’a da Asabar a kan sansanonin ‘yan gudun hijira biyu da ke fama da matsalar yunwa a arewacin Darfur da kuma babban birnin da ke kusa, inda rahotannin farko suka nuna cewa sama da mutane 100 ne suka mutu, ciki har da yara 20 da ma’aikatan agaji tara, a cewar wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya.
A halin da ake ciki kuma, ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ya sanar da samun karuwar adadin wadanda suka mutu a ranar Litinin, kamar yadda wasu majiyoyi na cikin gida suka tabbatar da hakan.