NIDCOM: An Ceto ‘Yan Nijeriya Sama Da 950 Daga Gidajen Kurkuku A Libya
Published: 26th, March 2025 GMT
Hukumar kula da ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen ƙetare (NIDCOM), ta bayyana cewa an kuɓutar da ‘yan Nijeriya 956 daga gidajen yarin Libya tare da mayar da su gida cikin watanni ukun farkon shekarar 2025.
Shugabar hukumar, Hon. Abike Dabiri-Erewa, ta ce waɗanda aka dawo da su sun haɗa da mata 683, maza 132, yara 87, da jarirai 54.
An samu nasarar mayar da su ne sakamakon haɗin gwiwa tsakanin NIDCOM, Hukumar ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) da kuma Hukumar Kula da Baƙin Haure da waɗanda rikici ya raba da matsugunansu (NCRMI).
A cewar sanarwar da NIDCOM ta fitar, an dawo da su ne kashi-kashi daga watan Janairu zuwa Maris 2025.
A ranar 28 ga Janairu, an dawo da mutum 152. A ranakun 11, 19, da 25 ga Fabrairu, an dawo da mutum 484. A ranakun 4 da 18 ga Maris, an dawo da mutum 320.
Dabiri-Erewa ta ƙara da kira ga ‘yan Nijeriya da su guji tafiya ƙetare ta ɓarauniyar hanya, musamman ta Libya, wacce ke fama da matsaloli da rikici.
Ta kuma jaddada cewa wajibi ne ‘yan Nijeriya su bi hanyoyin da doka ta tanada idan suna son yin hijira, domin guje wa hatsarin da ke tattare da tafiya ta haramtacciyar hanya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: yan Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Amurka Tana Shirin Dakatar Da Bada Kudaden Tallafi Don Samar Da Wasu Magunguna
Gwamnatin kasar Amurka tana shirin dakatar da bada kudade ga hukumar GAVI wacce take samar da alluran riga kafi don tallafawa kasashe masu tasowa daga ciki har da tarayyar Najeriya.
Jaridar Daily Trus ta Najeriya ta nakalto wata sanarwa daga hukumar USAID bayar inda take cewa gwamnatin shugaba Donal Trump yana son janye tallafin da kasarsa ke bayarwa don wannan shirin, wanda yake yakar cutar Malaria da wasu cututtuka a wadannan kasashe.
Labarin ya kara da cewa za’a dakatar da ayyukan samar da magunguna da alluran riga kafa har guda 5,341 idan an dakatar da tallafi, wanda yake cinye dalar Amurka biliyon 75 a ko wace shekara. A halin yanzu dai hukumar ta USAID ta bada dalar Amurla biliyon 48, don samar da wasu magungunan da alluran riga kafi n awannan shekarar.