Rikicin Masarauta: Duk mai ja da hukuncin Allah ba zai yi nasara ba — Sanusi II
Published: 26th, March 2025 GMT
Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II ya ce duk wani mai ƙoƙarin ja da hukuncin Allah to ba zai taba wanyewa lafiya ba.
Sanusi II ya ce duk wani mai ƙoƙarin kawo tazgaro ga zaman lafiyar Jihar Kano a ƙarshe aniyyarsa ce za ta koma kansa.
SSarkin ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan rediyon Premier da ke Kano, inda yake roƙon al’ummar jihar su zamo masu bin doka da oda, da kuma gudun aikata abubuwan da ka iya ta da hankali.
Kazalika ya bayyana masu ƙalubalantar kasancewarsa Sarki a matsayin masu yaƙi da nufin Allah, kuma a cewarsa hakan ba zai taɓa zame musu alheri ba.
Da yake jan hankalin Kanawan kan muhimmancin haƙuri da addu’a a wannan gaɓar, Sarkin ya ce turka-turkar da ake ciki game da masarautar Kano ba wai don shi ake yi ba, sai domin yaƙi da hukuncin Allah.
“Muna kira ga al’umma da su zamo masu bin doka da oda. Wannan rigimar ba da ni ake yinta ba, yaƙi ne da abinda Allah Ya ƙaddara.
“Ina roƙonku ku yi haƙuri ku dage da addu’a. Tabbas Allah Zai ci gaba da goya wa adalai baya.
“Wuta kuma ita ce karshen duk wani mai shirya wa Kano maƙarƙashiya. Allah Ya hana shi zaman lafiya.
“Muna roƙon Allah Ya kare kasarmu da rayukanmu. Da yardar Allah duk mai kokawa da hukuncin Allah ba zai gama da duniya lafiya ba,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Aminu Ado Bayero Sarkin Kano
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya da gwamnatin sojin Nijar sun sasanta
Gwmanatin Sojin Nijar ta sanar da cewa sun sasanta da gwamnatin Najeriya.
Hakan ta faru ne bayan ziyarar aiki da Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya kai birnin Yamai, fadar gwamnatin Nijar.
Bayan sanya hannu kan takardar, Ministan Harkokin Wajen Nijar, Bakary Yaou Sangare, ya bayyana cewa, “da ma Najeriya ’yan uwanmu ne, duk wanda ya ce zai raba Nijar da Najeriya, shi da kansa ya san ba gaskiya ba ne, abu ne na Allah. Allah Ne Ya haɗa wannan zumunta ka, babu wanda ya isa ya raba ta.”
Takwaransa na Najeriya, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa nan gaba Shugaba Bola Ahmed Tinubu za su gana da shugaban gwamnatin sojin Nijar, Janar Abdurrahman Tchiani, a matsayin ci gaban wannan daidaitawa.
Ya bayyana cewa yarjejeniyar da ƙasashen biyu suka sanya hannu a kai, ta zama, “darasi ga duk wasu ƙasashen duniya, domin yanzu an shiga wani lokaci da ake fama da tashe tashen hankali. To yanzu mu abin da a muka a tsakaninmu ya zama abin koyi.”