Aminiya:
2025-03-29@12:00:16 GMT

Ban sani ba ko zan tsaya takara a 2027 — Atiku

Published: 26th, March 2025 GMT

Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya ce kawo yanzu bai da ta cewa kan ko zai tsaya takarar shugabancin ƙasar a Zaben 2027.

Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira ta bidiyo a cikin shirin nan na Untold Stories tare da ɗan jarida Adesuwa Giwa Osagie wadda za a haska a yau Laraba.

Tsohon ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar PDP ya sanar da cewa za su yi maja da sauran jam’iyyun adawa domin ƙwace akalar jagoranci daga hannun Shugaba Bola Tinubu a Zaɓen 2027.

Kwamishinan Abba ya yi murabus bayan watanni 7 da naɗinsa Rikicin Masarauta: Duk mai ja da hukuncin Allah ba zai yi nasara ba — Sanusi II

A baya-bayan nan an ga yadda ’yan adawar ke haɗuwa da juna, kuma Atiku ya tabbatar wa duniya cewa suna tattaunawa domin ganin sun yi haɗakar da za ta ƙalubalanci jam’iyyar APC a zaɓen ƙasar mai zuwa.

Tun bayan wannan sanarwar ce ake ta cece-kuce kan ɗan takarar shugabancin ƙasar da wannan maja za ta tsayar.

Da yake amsa tambayar ko zai tsaya takara a 2027, Atiku ya ce “ba ni da masaniya a yanzu saboda abu na farko shi ne dole ne mu kafa wani tubali da ba a taɓa makamancinsa ba a tarihin siyasar ƙasar nan musamman tun bayan dawowa kan tafarkin dimokuraɗiyya.

Sai dai Atiku wanda ya yi takarar kujerar shugabancin Nijeriya sau shida bai ɗebe tsammanin cewa zai sake tsayawa takarar ba a 2027.

A cewar, “ba a taɓa samun lokacin da Nijeriya take buƙatar amintacce shugabanci mai nagarta kamar a yanzu ba.

“Mun taɓa yin makamanciyar wannan haɗaka ko maja a 2014. Kusan mu huɗu ko in ce uku, duk muka nemi takara, amma ɗaya ya yi nasara kuma duk muka mara masa baya har ya kai ga lashe zaɓe.

Atiku ya jaddada maganar da tsohon Shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya yi kwanan nan cewa dimokuraɗiyya ta ɗauko hanyar durƙushewa a ƙasar, “tabbas haka wannan batun yake.”

Atiku ya kuma bayyana damuwa kan alƙiblar da shugabancin Nijeriya ya fuskanta.

Ya ce “waɗanda suka zo bayan zamanin da muka yi, da yawa sun riƙe kujerar gwamna wasu kuma ta sanata, amma maimakon mu riƙa ganin ci gaba a shugabancin, sai dai koma baya kuma wannan lamari ne mai ban takaici.

Wazirin Adamawa ya kuma jefa ayar tambaya kan gaskiya da riƙon amanar ’yan Majalisar Tarayya musamman dangane da ayyana dokar ta ɓaci a Jihar Ribas da aka yi kwanan nan.

Dalilin da ban ɗauki Wike abokin takara ba a 2023

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma yi tsokaci kan dalilin da bai ɗauki Ministan Abuja, Nyesom Wike a matsayin abokin takararsa ba a Zaɓen 2023.

Galibi dai masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin wannan ne dalilin da jam’iyyar PDP ke ci gaba da fuskantar rikicin cikin gida tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu.

Ana kuma hasahen cewa wannan shawara da Atikun ya yanke ita ta ba shi matsala tare da haddasa masa rashin nasara a Zaɓen 2023, a yayin da Wike lokacin yana Gwamnan Ribas ya jagoranci wasu gwamnonin PDP da suka ƙulla adawa da jam’iyyar saboda zaɓin da Atiku ya yi na abokin takararsa.

Har daga bisani Wike ya riƙa bugun ƙirji cewa shi ne ya shiga ya fita ya yi wa Atikun bita da ƙulli kuma Shugaba Tinubu ya yi nasara a Jihar Ribas.

Sai dai duk da faruwar wannan, Atikun ya ce bai yi da na sanin rashin ɗaukar Wike a matsayin abokin takararsa ba.

Da yake kare matakin, Atiku ya ce ba zai manta yadda aka riƙa zargi da ƙalubalantarsa kan cewa bai nemi shawarwarin da suka dace ba wajen ɗauko abokin takararsa Peter Obi a lokacin Zaɓen 2019.

“A shekarar 2019, bayan na samu tikitin tsayawa takara a birnin Fatakwal. Sai na dawo kuma kai tsaye na wuce wurin maigidana, Shugaba Obasanjo, na sanar da cewa na samu tikitin takarar shugabancin ƙasa.

“Tambayar farko da ya yi min ita ce daga ina zan ɗauko abokin takara? Sai na ce ko dai daga Kudu maso Gabas ko kuma Kudu maso Yamma.

“Sai ya ce da ni na manta da Kudu maso Yamma saboda shi da ya fito daga yankin ya jagoranci ƙasar nan tsawon shekaru takwas. Ya ce da ni na ɗauko daga Kudu maso Gabas. Kuma na ce da shi an gama.

Atiku ya ce a lokacin ya sake neman shawarar Obasanjo kan abokin takarar da zai ɗauka, sai tsohon shugaban ƙasar ya ba da sunan Ngozi Okonjo Iweala, Darekta-Janar ta Hukumar Cinikayya ta Duniya wadda ta riƙe mukamin Ministar Kuɗi a zamanin Goodluck Jonathan.

“Sai na ce da shi Ngozi ba ’yar jam’iyyarmu ba ce. Idan na miƙa wa jam’iyyar sunanta ba za su amince ba. Sai ya ce da ni Soludo [tsohon Gwamnan CBN kuma Gwamnan Anambra na yanzu] fa? Shi ma na ce masa ba ɗan jam’iyyarmu ba ne saboda haka ko da na kai sunan shi ba za a amince ba.

“Sai ya ce da ni Peter Obi fa? Sai na ce masa tabbas Peter Obi ɗan jam’iyya ne. Haka kuwa aka yi.

“Na koma na shaida wa shugabannin jam’iyyarmu da safiya kuwa aka yi taron ba zan manta ba. Ga Uche Secondus, ga ni, ga Wike shi kansa da kuma Tambuwal, kusan mutum bakwai idan ban manta ba.

“Na shaida musu cewa ga abin da maigidana Obasanjo ya yanke. Akwai wani wanda bai gamsu da zaɓin nan ba, saboda ku ne shugabannin wannan jam’iyya kuma shugabannin ƙungiyar gwamnoni.

Atiku ya bayyana cewa duk cikinsu babu wanda ya nuna bai aminta ba, saboda haka aka sanar da Obi a matsayin abokin takararsa.

Sai dai Atiku ya ce daga bisani aka riƙa kalubalantar cewa bai nemi shawarwari sosai ba kuma hakan ce ta sanya da aka zo batun tsayar da abokin takara a Zaben 2023 na danƙa ragamar komai a hannun jam’iyya.

“Na ce da su, su kafa kwamitin da zai gabatar da mutum uku da suke ganin jamiyyar za ta tsayar a matsayin abokin takara.

Atiku ya ce bayan haka ne aka kawo sunayen mutum uku —  Gwamnan Delta mai ci a lokacin, Ifeanyi Okowa a matsayin zaɓin farko sai Wike na biyu sannan sai Gwamnan Akwa Ibom mai ci a lokacin, Udom Emmanuel a na uku.

Sai kawai na ɗauki zaɓin farko, ban ɗauki Wike ba saboda kawai Okowa shi ne zaɓin farko a jerin sunayen da suka gabatar.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Atiku Abubakar a matsayin abokin takara takarar shugabancin abokin takararsa abokin takarar ya ce da ni Atiku ya ce

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ta Gudanar Da Faretin Jiragen Ruwa A Tekun Farisa Da Kuma Tekun Caspian Don Raya Ranar Kudud Ta Duniya

Jiragen ruwan yaki na dakarun juyin juya halin musulunci  IRGC a nan Iran, kanana da manya-manya, har’ila yau da na masu sa kai sun gudanar da faretin jiragen ruwan yaki don raya ranar Kudus ta duniya kwana guda kafin ranar.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto dubban  jiragen yaki da na masu sa kai a tekun Farisa da ke kudancin kasar da kuma tekun Caspian da ke arewacin kasar suna jerin gwano a cikin ruwayen yankunansu don raya wannan ranar.

Dakarun IRGC sun gudanar da wannan atisai ne a jiya Alhamis, don nuna goyon bayansu ga Falasdinwa musamman a Gaza, wadanda a halin yanzu, sojojin HKI sun yi masau kawayya, sun hana shigowar abinda da abinsha  cikin yankin sama da wata gusa, sannan suna binsu suna kashewa.

Majiyar dakarun IRGC ta bayyana cewa sama da jiragen ruwa da kwale-kwale kimani 3,000 ne suka fito don tallafawa falasdinawa musamman a Gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan, wadanda sojojin yahudawa suka kashewa a ko wace rana.

Labarin ya kara da cewa, a kudancin kasar an baje kolin katafaren jirgin ruwa mai daukar jirage yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa, mai sun a ‘shahida beheshti’, jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa suna sauka su kuma tashi a kan wannan jirgin yakin.

HKI dai wacce take samun tallafin kasashen yamma musamman Amurka suna mamaye da kasar Falasdinu fiye da shekaru 70 a halin yanzu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jami’an Tsaro A Jihar Kano Na Tarayyar Najeriya Sun Hana Bikin Dabar NA Sallar Bana
  • Tinubu zai sake zama shugaban ƙasa a 2027 — Akpabio
  • Jihad Islami: Ranar Quds Dama Ce Ta Hadin Kai Tsakanin Al’umma
  • Ana Gudanar Da Tarukan Ranar Quds Ta Duniya A Wannan Juma’a
  • Iran Ta Gudanar Da Faretin Jiragen Ruwa A Tekun Farisa Da Kuma Tekun Caspian Don Raya Ranar Kudud Ta Duniya
  • NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Musulmi Su Yi Kafin Da Kuma Ranar Sallah
  • Wani abu kan Zakkatul Fidir da Sallar Idi
  • Zamu Tabbatar Ingantuwar Depon Sojoji Na Zaria – Ministan Tsaro Badaru
  • Nijar : An nada Janar Tiani, a mukamin shugaban rikon kwarya
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [19]