Aminiya:
2025-03-29@13:36:03 GMT

Gwamnatin Kano za ta hukunta masu shigar banza a bikin Sallah

Published: 26th, March 2025 GMT

Gwamnatin Kano ta sha alwashin hukunta masu shigar banza ko cudanya maza da mata a lokacin bukukuwan Sallah Karama da za a yi.

Gwamnatin ta bayyana hakan ne ta bakin shugaban Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Kano, Abba Almustapha a wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun kakakin hukumar Abdullahi Sani Sulaiman, inda ta ce matakin yunkuri ne na gwamnatin domin tsaftace yadda gidajen wasanni da kidan DJ ke shagalin bikin Sallah.

Ban sani ba ko zan tsaya takara a 2027 — Atiku Kwamishinan Abba ya yi murabus bayan watanni 7 da naɗinsa

“A kokarin ta na yaki da rashin da’a tare tsaftace yadda gidajen wasanni da masu kidan DJ za su gudanar da shagalin bikin sallah a Kano, Hukumar tace fina-finai da Dab’i karkashin jagorancin Abba El-mustapha ta bayyana shirinta na saka kafar wando daya da duk wani gidan wasa ko mai kidan DJ da aka samu da rashin da’a a yayin gudanar da bikin sallah a Jihar.

Hukumar ta shirya wata tawaga ta musamman da za ta kewaya gidajen wasannin a bikin sallah karkashin kulawar Alh. Abubakar Zakari Garun Babba Daraktan Dab’i na Hukumar, domin sanya ido da tabbatar ba a bai wa masu shigar banza ko shaye – shaye damar shiga gidajen wasannin ba.

“Haka kuma, hukumar ta hana hada maza da mata a guri daya a yayin bikin sallar. Tawagar za ta yi aiki ne dare da rana daga ranar daya ga sallah har zuwa lokacin da za’a kammala bikin sallar domin cimma nasarar aikin da ta sanya a gaba.”

El-mustapha ya kuma yi gargadi ga masu gidajen wasanni da masu sana’ar DJ, da su yi biyayya ga dokokin hukumar sau da kafa domin gujewa fushinta.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Hukumar Tace Fina finai da Dab I ta Kano Kannywod

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Musulmi Su Yi Kafin Da Kuma Ranar Sallah

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Lokutan sallah su ne lokuta na farin ciki, godiya ga ni’imar Allah, da kuma ibada.

A wannan lokaci, yana da muhimmanci a tabbatar da ayyukan da ake aikatawa sun kasance masu inganci da dacewa da koyarwar addini.

NAJERIYA A YAU: Halin Da Matasa Suka Tsinci Kansu A Najeriya NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri

Amma mene ne ya kamata musulmi su yi kafin da kuma ranar sallah?

Ta wacce hanya za a tabbatar da zaman lafiya da tsari yayin bukukuwan sallah?

Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari kan muhimman abubuwan da Musulmi ya kamata su aikata kafin da kuma lokacin sallah.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yansanda Sun Hana Hawan Sallah A Kano Saboda Tsaro
  • ’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano
  • Sallah: Hadimin gwamnan Sakkwato ya bai wa magoya bayan APC kyautar N22m
  • NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Musulmi Su Yi Kafin Da Kuma Ranar Sallah
  • Yobe Ta Bayyana Ɗaukar Matakan Tsaro A Lokacin Bikin Sallah
  • Sallah: ’Yansanda Sun Yi Alƙawarin Tabbatar Da Tsaro A Kano
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bada Hutun Sallah Karama Ta 2025/1446
  • Sarkin Kano Na 15 Ya Soke Hawan Daba Saboda Matsalar Tsaro
  • Aminu Ado Ya Soke Hawan Sallah Don Tabbatar Da Zaman Lafiya A Kano
  • Sallah: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Litinin Da Talata A Matsayin Hutu