’Yan fashi 4 sun mutu yayin tsere wa ’yan sanda a Nasarawa
Published: 26th, March 2025 GMT
Wasu mutane huɗu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun mutu a sakamakon hatsarin mota a Jihar Nasarawa.
Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar SP Nansel Rahman, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce lamarin ya auku ne lokacin da ‘yan fashin ke ƙoƙarin tserewa jami’an.
Gidauniyar Zakkah ta raba wa marayu 100 kayan sallah a Gombe Kantoman Ribas ya naɗa sabon Sakataren Gwamnati“A ranar 25 ga watan Maris ne rundunarmu ta samu wani kiran gaggawa kan wasu ‘yan fashi na tsaka da ta’asa a bayan filin wasa na ƙaramar hukumar Keffi.
“Bayan samun kiran ne kwamishinan ‘yan sanda Shettima Jauro Mohammed ya ba da umarnin bin bayan ‘yan fashin nan take.
“Suna cikin guje mana ne a cikin motar da suka sace ƙirar Toyota Camry suka yi haɗari a babban titin Abuja-Keffi.
“Jami’anmu da ke ofishin ‘yan sanda na Goshen ne suka kwashe su zuwa asibiti, a nan mutum huɗu suka mutu.
“Ɗayan da ya rage kuma na hannunmu likitoci na bashi kulawa.
Binciken ‘yan sanda dai ya kai ga gano wasu kayan da ‘yan fashin suka sata da suka haɗa wayoyin hannu 12, agogunan hannu, sai makamai da suka haɗa da manyan wuƙaƙe biyu, sukundireba, da kuma layu.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Ta Bukaci Jami’an Tsaro Mata Su Rika Sanya Hijabi Yayin Aiki
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da amfani da Hijabi ga jami’an tsaro mata a fadin jihar.
Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse.
A cewarsa, majalisar ta bayar da umarni ga kamfanonin tsaro guda uku da ke aiki a jihar, su bai wa jami’an tsaro mata daga cikin matasa 9,969 da aka dauka aiki, damar sanya Hijabi yayin aiki, a matsayin girmamawa ga addini da al’adu.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, wannan matsaya ta biyo bayan rahoton da kwamitin majalisar kan tsaron makarantu, asibitoci da kotuna ya gabatar, kuma aka sake jaddada kudurin gwamnatin na tabbatar da tsarin aiki mai cike da mutuntaka, da daidaito.
Ya ce, majalisar zartarwar ta kuma amince da kaddamar da makon kirkira da kere-kere na jihar (JISCIW) daga shekarar 2025.
Ya jaddada cewa, wannan tsari na nuna jajircewar gwamnatin wajen bunkasa basira da hazakar matasa, da kuma inganta kirkire-kirkire da tunani mai zurfi a fadin jihar.
Sagir ya bayyana cewa, JISCIW zai kara zaburar da matasa a fannoni daban-daban kamar fasaha, zane, kasuwanci da kuma harkokin fasaha.
Ya kara da cewa, majalisar ta amince da fitar da sama da Naira miliyan 516 domin sayen tikitin jirgi ga daliban jihar Jigawa 185 da ke karatu a fannin likitanci da kimiyyar kiwon lafiya a Jami’ar Near East dake kasar Cyprus, domin shirye-shiryen zangon karatu na shekarar 2024/2025.
Kwamishinan ya kara da cewa, wannan tallafi ya nuna yadda gwamnatin ke ci gaba da daukar nauyin ilimi da jin dadin daliban da ke karatu a kasashen waje, musamman a muhimman fannoni kamar likitanci da kiwon lafiya.
Usman Muhammad Zaria