Ministan tsaro ya yi alƙawarin kawo sauyi a cibiyar horar da sojoji
Published: 26th, March 2025 GMT
Ministan Tsaro, Mohammed Abubakar Badaru, ya ziyarci Cibiyar Horar da Sojoji da ke Zariya, inda ya yi alƙawarin samar da ƙarin kayan aiki da ci gaba da inganta horon kuratan sojoji domin su dace da buƙatun zamani.
A lokacin ziyarar, Ministan ya bayyana gamsuwarsa da horon da kurata na kashi 88 ke samu, inda ya jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya na bunƙasa kayan horo da samar da ingantattun makamai da kayan aiki ga dakarun sojoji.
Badaru ya yi alƙawarin tuntuɓar Gwamnatin Jihar Kaduna, domin kammala ginin Makarantar Sakandaren Chindit, wadda ba a kammala ta ba tsawon lokaci.
Ya kuma bayar da tabbacin samar wa Makarantar Firamare ta Chindit kayan aiki domin inganta ilimin ’ya’yan sojojin da ke barikin.
Baya ga haka, ministan ya amince da samar da rijiyoyin burtsatse a barikin, domin shawo kan matsalar ƙarancin ruwa da ake fuskanta a Depot Zariya.
A jawabinsa na maraba, Kwamandan Depot, Manjo Janar Ahmadu Mohammed, ya gode wa ministan bisa wannan ziyarar, tare da bayyana yadda Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ke ba su goyon baya domin magance matsalolinsu.
Ya kuma bayyana cewa za su ci gaba da samar da ƙwararrun sojoji masu kishin ƙasa da jajircewa.
Ziyarar ministan ta samu rakiyar manyan jami’an tsaro, ciki har da Babban Sakataren Ma’aikatar Tsaro, Jakada Gabriel Aduda, da Manjo Janar Ahmed Jubrin (mai ritaya), da kuma Birgediya Janar Aminu Garba.
Hakazalika, wasu manyan hafsoshin soji irin su Kwamandan Armed Forces Command and Staff College, Air Marshal Hassan Alhaji, da Kwamandan Makarantar Motsa Jiki ta Sojojin Najeriya, Birgediya Janar Owoicho Ejiga, na cikin tawagar.
Ziyarar na daga cikin ƙoƙarin ministan na ganin an inganta cibiyoyin horon sojoji domin tabbatar da nagartar jami’an tsaro a Najeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Alƙawari Cibiyar Horar Da Sojoji kayan aiki Ministan tsaro Mohammed Badaru Zariya
এছাড়াও পড়ুন:
Ba a taɓa Dimokraɗiyya mai tsafta a Najeriya kamar mulkin Tinubu ba – Matawalle
Karamin Ministan Tsaro a Najeriya Bello Matawalle, ya caccaki masu sukar lamirin Shugaban Kasa Bola Tinubu game da nuna wariya ga yankin Arewacin Najeriya.
Matawalle ya ce Tinubu kadara ne ga Arewa kuma ba shi da fatan da ya wuce ganin ya magance matsalolin da suka addabi yankin kafin 2027.
Cikin wani jawabi da mai taimaka masa kan sha’anin siyasa Ibrahim Danmaliki Gidan Goga ya fita, Matawalle ya ce ba a taba samun lokacin da ake yin dimokradiyya mai tsafta kamar a zamanin Bola Tinubu ba.
’Yan Najeriya miliyan 150 sun samu ingantacciyar wutar lantarki – Minista
Ya ce duk masu kushe salon mulkinsa kawai suna huce haushin rashi ne da yada farfaganda da karairayi.
“Mutanen Arewa suna da wayewar da sun fi karfin a yaudare su domin cimma wata manufar siyasa. Akwai bukatar mu hada kai waje daya kada mu yarda a yaudare mu.” Inji Matawalle.
Ministan ya ce kamata ya yi a gode ma Tinubu saboda yadda yake inganta yankin Arewa da tsaro kuma ana ganin ci gaba musamman yankin da ya fito na Sokoto-Kebbi-Zamfara.
Bugu da kari ya yaba ma ayyukan ci gaban da yake kawo wa yankin musamman yadda ake shimfida tituna da kokarin kawo ci gaba ga yankin.