JIBWIS Ta Raba Kayan Abinci Na Kimanin Naira Miliyan 9 Ga Marayu
Published: 26th, March 2025 GMT
Kwamitin tallafawa marayu da masu karamin karfi na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Ikamatis Sunnah dake karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa ya tallafawa gidajen marayu da masu karamin karfi da kayan abinci na kusan naira miliyan 9.
Shugaban kungiyar Sheikh Hassan Sabo Musa ya bayyana hakan yayin rabon kayan da aka gudanar a karamar hukumar Babura.
Yace, an sami gudunmawar kudade da kayan abinci daga al’umma da kungiyoyi.
Sheihk Hassan Musa ya kara jadadda bukatar cewar, ya zama wajibi a rika jibintar al’amuran marayu domin samun falala daga Allah.
A jawabinsa, shugaban kwamitin tallafawa marayu, Malam Nura Sale ya ce wannan shine karo na goma Sha biyu na shirin.
Ya godewa wadanda suka bayar da gudunmwar da ‘yan kwamitin da wadanda suka tallafa aka sami nasarar aikin.
Wakilinmu ya ruwaito cewa an ba gidajen marayu 273 shinkafa, yayin da masu karamin karfi 340 aka basu taliya.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Sakkwato Ta Siyawa ‘Yan Gudun Hijira Gidan Miliyan 100
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp