Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4
Published: 26th, March 2025 GMT
Majalisar Wakilai ta ɗauki mataki na gaba wajen ƙirƙirar sabbin jihohi huɗu a Najeriya.
’Yan majalisa sun tattauna tare da amincewa da karatu na biyu na ƙudirorin da ke neman kafa jihohin Oke-Ogun, Ijebu, Ife-Ijesa, Tiga, Orlu, da Etiti.
Gidauniyar Daily Trust da WRAPA sun ’yanta fursunoni 21 a Kaduna da Katsina Kakakin ’yan sandan Taraba, Abdullahi Usman, ya rasuWaɗannan ƙudirori na daga cikin yunƙurin sauya kundin tsarin mulkin 1999.
Shugaban masu rinjaye na majalisa, Hon. Julius Ihonvbere, wanda ya gabatar da ƙudirorin, ya jaddada muhimmancinsu.
“Waɗannan ƙudirori suna nuna buƙatun yankuna daban-daban na ƙasa domin samar da ingantaccen shugabanci da rarraba albarkatu cikin adalci,” in ji shi.
Mataimakin Kakakin Majalisa, Benjamin Kalu, wanda ya jagoranci zaman, ya jagoranci kaɗa ƙuri’ar murya inda ƙudirorin suka samu amincewa.
An tura su zuwa kwamitin majalisa kan sauya kundin tsarin mulki domin ci gaba da nazari.
Ɗaya daga cikin masu ɗaukar nauyin ƙudirin, Hon. Ghali Mustapha Tijani, ya ce, “Kafa Jihar Tiga zai kusanto da gwamnati ga jama’a tare da haɓaka ci gaba.”
Ana buƙatar amincewar majalisun dokokin jihohi da na ƙasa kafin ƙirƙirar sabbin jihohin a Najeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: karatu Majalisar Wakilai Tsallakewa
এছাড়াও পড়ুন:
Girgizar ƙasa ta hallaka sama da mutum 1000 a Myanmar
Gwamnatin Soji ta Myanmar, ta bayyana cewa mutum 1,002 sun rasa rayukansu sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfi da ta auku a ranar Juma’a.
Sama da mutum 2,000 sun jikkata, kuma ana ci gaba da ceto waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin gine-ginen da suka rushe.
Mutum 14 sun shiga hannu kan kisan ’yan Arewa a Edo An kashe mutum 10 a wani sabon hari a FilatoJami’an agaji sun ce girgizar ƙasar ta fi shafar birnin Mandalay, inda asibitoci suka cika maƙil da waɗanda suka jikkata.
Shugaban mulkin soji na Myanmar, ya nemi taimakon ƙasashen duniya, amma ana fargabar yaƙin basasa da ke ci gaba a ƙasar zai hana ayyukan jin-ƙai tafiya yadda ya kamata.
Hukumar kare haƙƙin bil adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ta ce Myanmar na cikin yaƙi tun shekaru huɗu da suka wuce, wanda ya haifar da zargin cewa dakarun soji na tsare ɗaruruwan mutane.