Aminiya:
2025-03-29@18:25:24 GMT

Mutum 2 sun rasu, wani ya ji rauni a hatsarin mota a Kano

Published: 26th, March 2025 GMT

Aƙalla mutum biyu ne suka rasu, yayin da wani ya jikkata a wani hatsarin mota da ya auku kusa da Sinimar Eldorado da ke kan titin zuwa Filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano.

Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta tabbatar da faruwar lamarin.

Gidauniyar Daily Trust da WRAPA sun ’yanta fursunoni 21 a Kaduna da Katsina Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu

Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:15 na safiyar yau Laraba, inda ya haɗa wata babbar mota ƙirar DAF da babur ƙirar Jincheng.

Mai magana da yawun FRSC, Abdullahi Labaran, ya ce tuƙin ganganci ne ya haddasa hatsarin.

“Daga cikin mutum shida da hatsarin ya shafa, biyu sun rasu, yayin da ɗaya ya samu munanan raunuka,” in ji shi.

Jami’an FRSC sun isa wajen da hatsarin ya auku cikin minti uku sannan suka kai wanda ya jikkata zuwa Asibitin Murtala Muhammad domin samun kulawar gaggawa.

An kuma kai gawarwakin waɗanda suka rasu Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.

An miƙa motocin da sauran kayayyakin da aka ƙwato zuwa ofishin ‘yan sanda na Gwagwarwa domin ci gaba da bincike.

FRSC, ta shawarci direbobi da su bi dokokin hanya tare da yin tuƙi cikin taka-tsantsan don kaucewa irin waɗannan haɗura.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hatsarin mota

এছাড়াও পড়ুন:

Cutar sanƙarau ta yi ajalin mutum 3 a Gombe

Gwamnatin Jihar Gombe, ta tabbatar da mutuwar mutum uku daga cikin 33 da suka kamu da cutar sanƙarau a jihar.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Habu Dahiru ne, ya bayyana hakan yayin ƙarin haske game da ɓullar cutar a jihar.

Majalisa ta janye ƙudirin tuɓe wa matakaimakin shugaban ƙasa da gwamnoni rigar alfarma Lakurawa sun kashe jami’an Kwastam 2 a Kebbi

Yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis, ya bayyana cewa an samu rahoton mutum 53 da ake zargi sun kamu da cutar a ƙananan hukumomi hudu: Kaltungo, Yamaltu Deba, Billiri, da Gombe.

A cewarsa, an tabbatar da mutuwar mutum uku daga ƙananan hukumomin Kaltungo, Yamaltu Deba, da Billiri.

A Shongom kuwa, daga cikin mutum huɗu da ake zargi sun kamu da cutar, an tabbatar da uku na ɗauke da ita.

Sai kuma ƙananan hukumomin Dukku da Nafada, inda aka samu mutum ɗaya kowanne, amma ba a tabbatar da sun kamu ba.

Kwamishinan, ya ce gwamnatin Gombe, ta samar da magunguna kyauta domin kula da masu cutar a cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a ƙananan hukumomi 11 na jihar.

Ya bayyana cewa alamomin cutar sun haɗa da zazzabi, ciwon wuya, da ciwon kai mai tsanani.

Ya kuma shawarci jama’a da su kiyaye tsafta, guje wa zama a ɗakuna marasa iska, da kuma nisantar masu alamomin cutar domin hana yaɗuwarta.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Girgizar ƙasa ta hallaka sama da mutum 1000 a Myanmar
  • Mutum 14 sun shiga hannu kan kisan ’yan Arewa a Edo
  • An kashe mutum 10 a wani sabon hari a Filato
  • An cafke mutum 19 bayan arangama tsakanin sojoji da ’yan shi’a a Abuja
  • Girgizar ƙasa ta kashe mutum 150 a Myanmar da Thailand
  • Yadda Ake Fitar Da Zakkar Fidda Kai Da Sallar Idi
  • Cutar sanƙarau ta yi ajalin mutum 3 a Gombe
  • Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutane 2 A Kano – FRSC
  • Hadimin Gwamnan Kano Tanka Galadanci ya rasu
  • An kama mutum 3 kan zargin sata da ƙone gidan bature a Gombe