Jagoran Juyin Musulunci Ya Amince Da Yin Afuwa Ga Wasu Fursunoni Masu Yawa
Published: 26th, March 2025 GMT
Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya amince da bukatar ma’aikatar shari’a na yin afuwa ga wasu fursunoni sannan kuma da rage yawan shekarun wasu na zaman gidan kurkuku.
Yin afuwar ga fursunonin dai ya zo saboda shiga sabuwar shekarar hijira shamshiyya ta 1404 da kuma karatowar karamar salla ra 1446.
Shugaban ma’aikatar shari’a ta Iran Hujjatul-Islam Wal Muslimin Gulam Muhsin Eji ne ya gabatar da bukatar neman afuwar ga fursunonin ta mutane 1526, wanda kuma ya sami amincewar jagoran.
A kowace shekara a lokutan bukukuwan addini da nasa ana yi wa fursunoni masu kananan laufuka afuwa, yayin da ake rage wa wasu tsawon wa’adin zamansu a gidan kurkuku.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Ta Bada Hutun Sallah Karama Ta 2025/1446
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Litinin 31 ga watan Maris da Talata 1 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun karamar Sallah.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida wadda babbar sakatariyar ma’aikatar Magdalene Ajani ta sanya wa hannu.
A cikin sanarwar, ministan harkokin cikin gida na Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo ya buƙaci dukkanin Musulmai su rungumi tausayawa da karamci da zaman lafiya, inda ya jaddada muhimmancin nuna soyayya da yafiya da haɗin kai domin gina alumma mai cike da zaman lafiya.
Ya kuma buƙaci alummar Musulmi su yi wa Najeriya addu’ar ɗorewar zaman lafiya da samun ci gaba, kuma ya yi kiran gudanar da bukukuwan sallah lafiya.