HKI Ta Kai Hare-hare A Falasdinu Da Kasar Lebanon
Published: 26th, March 2025 GMT
Sojojin mamayar HKI sun kai sabbin hare-hare a wasu yankuna na gabashin kasar Lebanon, adaidai lokacin da take ci gaba da kai wa yankin yammacin kogin Jordan wasu gare-haren.
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa; Sojojin mamayar sun kame Falasdinawa 5 a garin al-Khalil dake kudancin yammacin kogin Jordan.
A garin Bireh da wasu yankuna na Ramallah, sojojin mamayar sun kai wasu hare-haren a yau Laraba.
A cikin watannin bayan nan, sojojin HKI sun rushe gidajen Falasdinwa 79 a cikin yankin yammacin kogin Jordan, tare da tilastawa mazaunan gidajen kusan 40,000 yin hijira.
A ranar 22 ga watan Maris ne dai jiragen yakin HKI su ka kai hare-hare a gargruwan Lebanon da su ka hada, Nabi Shit, Hermel, da wasu garuruwan da suke a yankin Bika. Haka nan kuma sun kai wasu hare-haren a garin Deir Qanun.
Tun daga fara yaki akan Gaza, sojojin HKI sun kashe Falasdinawan da sun haura 50,000, yayin da wani adadin da ya kai mutane113,000 su ka jikkata.
A can yankin Gaza ma, sojojin na HKI suna cigaba da kai hare-hare wanda ya yi sanadiyyar samun shahidai da dama.
Hare-haren na sojojin mamaya ya shafi garin Khan-yunus dake kudancin Gaza, haka nan kuma a garin Rafaha dake kan iyaka da kasar Masar.
Da safiyar yau Laraba kadai Falasdinawa 11 ne su ka yi shahada, daga cikinsu da akwai kananan yara 5.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Yi Allawadai Da Sabon Harin HKI A Kasar Lebanon
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bakin kakakinta Dr. Isma’ila Baka’i, ta yi tir da sabbin hare-haren da HKI ta kai wa kasar Lebanon a daidai lokacin da ake bikin ranar Kudus.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na kasar ta Iran ya bayyana cewa; Abinda HKI ta yi keta tsagaita wutar yaki ne,wanda abin a yi tir da shi ne.
Haka nan kuma ya yi ishara da nauyin da ya rataya akan wuyan Majalisar Dinkin Duniya da kuma sauran kasashen da suke cikin sa-ido da ‘yarjeneniyar tsagaita wutar yaki, haka nan kuma ya yi kira zuwa ga kungiyoyin kasa da kasa da su dauki mataki na gaggawa domin kawo karshen maimaita keta tsagaita wutar yaki da ‘yan sahayoniyar suke yi.
Har ila yau, kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya ce; “ Dalilin da ‘yan sahayoniya su ka bijiro da shi na kai wa Lebanon hari,ba zai zama karbabbe ba, don haka wajibi ne ga kungiyoyin kasa da kasa da su dauki matakin yadda ‘yan sahayoniyar suke keta wutar yaki a cikin Gaza, Lebanon da kuma Syria.
Dr. Baka’i ya bayyana abinda HKI take yi da cewa, baraza ce ga zaman lafiya da sulhu na duniya.
Tun bayan tsagaiwa wutar yaki a kasar Lebanon, HKI tana keta ta a duk lokacin da ta so, kamar kuma yadda ta kafa sansanoni biyar da ta girke sojojinta a ciki.