Aminiya:
2025-03-30@13:14:58 GMT

Aminu Ado ya soke hawan salla don gudun rikici a Kano

Published: 27th, March 2025 GMT

Sarkin Kano 15, Aminu Ado Bayero, ya soke shirinsa na gudanar da bikin hawan salla bayan shawarwari da dattawa da malaman addini suka ba shi.

Ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan buƙatar tabbatar da zaman lafiya a jihar, biyo bayan shiga ruɗani da jama’a suka yi.

Hadimin Gwamnan Kano Tanka Galadanci ya rasu Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4

Wannan na zuwa ne yayin da aka shiga ruɗani a Kano saboda rikicin masarauta, biyo bayan mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

Tun farko, duka sarakunan biyu – Sanusi II da Aminu Ado Bayero, sun shirya gudanar da hawan salla, lamarin da ya haddasa fargaba a tsakanin al’umma.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Laraba, Sarki Aminu, ya ce ya ɗauki matakin ne bayan jin ra’ayin malamai da dattawa.

“Malamai da dattawa sun shawarce mu, kuma muna mutunta su. Don haka, bayan nazari tare da majalisar masarauta, mun yanke shawarar cewa mun janye domin zaman lafiya,” in ji shi.

Idan za a tuna, a makon da ya gabata ne, Aminu Ado, ya aike wa ’yan sanda takardar neman izinin gudanar da hawan salla, bayan da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci Muhammadu Sanusi II, ya shirya yin hawan salla a bana.

Sarkin ya jaddada cewa bikin hawan salla ba abu ne da ya zama wajibi ba idan zai iya haddasa rikici da asarar rayuka.

“Idan akwai fargabar cewa hawan salla zai haddasa tashin hankali da asarar rayuka ko dukiyoyi, to, yana da kyau a daina,” in ji shi.

A gefe guda, al’ummar Kano sun nuna damuwa kan yadda rikicin masarautar ke ci gaba da yin tasiri a rayuwarsu.

Ana sa ran wannan matakin zai rage fargabar da ake ciki, tare da tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kano.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Aminu Ado Bayero Fargaba gwamna hawan salla Rikicin Masarauta Ruɗani Soke Hawan Salla hawan salla

এছাড়াও পড়ুন:

Jami’an Tsaro A Jihar Kano Na Tarayyar Najeriya Sun Hana Bikin Dabar NA Sallar Bana

Jami’an tsaro a tarayyar Najeriya a birnin Kano sun haramta daban da aka saba yi a karshen watan azumi a birnin.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto Jami’an tsaron kasar suna bada wannan sanarwan ne bayan da sarki na 15 Wato Aminu-  Ado Bayero ya bada sanarwan janye daban da ya shirya gabatarwa a kwanakin salla Karamah.

Shugaban Jami’an tsaron ya bayyana haka ne a wani taron yan jarida da ya gabatar a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa baza su amince da gudanar da taron Durba a karamar sallah a wannan shekara ba.

Kakakin yansada na jihar Kano Haruna Kiyawa, ya sanya sanarwan a shafinsa na Facebook.

Kafin haka aranar 18 ga watan Maris da muke ciki ne gwamna Abba Yusuf na Jihar Kano ya umurce masarautar Kano ta shirin gudanar da wannan bikin kamar yadda ta saba. Ya gwamnatinsa ba zata amincewa masu adawa su kawo cikas a cikin shirin ba. 

Gwamnan ya yi wa mutanen alkawali kan cewa Jami’an tsaro zasu tabbatar da tsaro da zaman lafiya a lokacin bikin Dubar, mai magana da yawan gwamnan jihar ya kara jaddadawa.

Sai da Mr Kiyawa ya bayyana cewa sun dauki makakin hana kilisa ko Durbar kwata-kwata a jihar ne bayan sun yi nazararin harkokin tsaro a jihar suka kuma ga cewa ba za su amince da duk abinda zai tada hankalin mutanen jihar ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Talakawa su girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin Musulmi
  • Bayan Hukuncin ‘Yansanda, Sarki Sanusi II Ya Soke Hawan Sallah
  • Yau Lahadi Ce Take Salla A Kasashen Larabawa Da Dama
  • Dalilin da Aminu Bayero ba zai iya jagorantar hawan Sallah ba — Kurawa
  • Rikici Ya Turnuke Jam’iyyar SDP A Yayin Da Aka Samu Shugabanni Bangare Biyu A Kogi
  • Rikici ya ɓarke bayan wata mata ta mari ɗan sanda a Saudiyya
  • Jami’an Tsaro A Jihar Kano Na Tarayyar Najeriya Sun Hana Bikin Dabar NA Sallar Bana
  • ‘Yansanda Sun Hana Hawan Sallah A Kano Saboda Tsaro
  • ’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano
  • Aminu Bayero ya soke hawan Sallah