Kantoman Ribas ya dakatar da hadiman Fubara
Published: 27th, March 2025 GMT
Kantoman Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya dakatar da dukkanin masu riƙe da muƙaman siyasa da jami’an gwamnatin jihar nan take.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Ibas, ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bisa izinin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba shi.
Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin da Talata ranakun hutun sallah Ministan tsaro ya yi alƙawarin kawo sauyi a cibiyar horar da sojojiWaɗanda abin ya shafa sun haɗa da Sakatare na Gwamnatin jihar, Shugaban Ma’aikata, Kwamishinoni, shugabannin hukumomi, da masu ba da shawara na musamman.
Ya umarci duk waɗanda abin ya shafa da su miƙa ragamar ayyukansu ga sakatarorin ma’aikatunsu.
Ya ce hukumomin da babu sakatare, sai a bai wa babban darakta mafi girma ko shugaban gudanarwa.
Wannan umarni ya fara aiki daga ranar Laraba, 26 ga watan Maris, 2025.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: dakatarwa Muƙaman Siyasa umarni
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Yobe ta sayo hatsi don tunkarar kakar bana
Gwamnatin Jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ta sayo ton 2,000 na hatsi iri-iri domin ƙarfafa samar da abinci da kuma tabbatar da shirin tunkarar kakar bana a matsayin gudun ko ta kwana.
A cikin wata sanarwa da Yusuf Ali, mai bada shawara ta musamman kan harkokin dabarun sadarwa na zamani (SSA) ga gwamna Buni ya ce, Kwamishinan ma’aikatar noma da albarkatun ƙasa, Ali Mustapha Goniri, ya kai ziyarar duba irin hatsin a shagunan bunƙasa noma na jiha da ke kan titin Gujba da ke Damaturu.
’Yan Najeriya miliyan 150 sun samu ingantacciyar wutar lantarki – Minista ISWAP sun ruguza gadar Mandafuma a BornoDa yake zantawa da manema labarai a yayin ziyarar, Ali Mustapha ya bayyana kyakkyawan fata game da shirin, inda ya jaddada cewa za a raba hatsin ga jama’ar Yobe a cikin gaggawa ko kuma lokacin bazara domin rage matsalar ƙarancin abinci.
Baya ga hatsin, Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati ta sayo nau’o’in sinadarai iri-iri domin tallafa wa manoman rani da kayan lambu.
Ya kuma bayyana shirin raba irin rogo ga manoma a fadin jihar, da nufin farfaɗo da noman na rogo lura da amfanin da ake yi da ita ta fuskoki iri-iri na abinci har ma da sarrafa ta da ake yi ya zuwa garin fulawa don yin abubuwa da ita.
Kwamishinan ya yabawa gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni, bisa jajircewa da goyon baya da take bayarwa wajen bunƙasa harkar noma a Jihar Yobe.
Tawagar binciken ta haɗa da babban sakataren ma’aikatar, Barista Muhammed Inuwa Gulani da daraktoci da sauran jami’an ma’aikatar.
Wannan shiri ya ƙara jaddada ƙudirin gwamnatin Jihar Yobe na inganta samar da abinci da kuma baiwa manoma damar bunƙasa harkokin su na noma da nufin samar da ishasshen abinci a faɗin jihar.