Sudan ta Kudu : Ana tsare da Riek Machar a wani gida
Published: 27th, March 2025 GMT
Bayanai daga Sudan ta kudu na nuni da cewa ana tsare damataimakin shugaban kasar na farko Riek Machar a wani gida, lamarin da MDD ta nuna matukar damuwa na yiwuwar komawar kasar wani yakin basasa.
Rahotanni sun ce a yammacin jiya Laraba jami’an tsaron Sudan ta Kudu sun tsare Riek Machar, kamar yadda kakakinsa ya sanar.
Ba a fayyace ainihin dalilin wannan tsarewar da kuma tasirinta ga dorewar yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattabawa hannu a shekarar 2018 ba.
Tun a farkon watan Maris ne dai ake ta rade-radin kame Riek Machar, lokacin da rikicin yankin Upper Nile da ke arewa maso gabashin kasar ya kai ga kame wasu jami’an jam’iyyarsa a Juba.
tsare Mista Machar madugun ‘yan adawa na kasar na jefa shakku sosai kan shirin samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu a cewar masana.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Riek Machar
এছাড়াও পড়ুন:
Kada Kanawa su bari rigingimun siyasa su hana su zaman lafiya — Shettima
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya shawarci Kanawa kan kada su bari bambance-bambancen aƙidu na siyasa su zama silar hana su zaman lafiya da haɗin kai.
Ya faɗi hakan ne a jawabinsa lokacin da ya je yi wa Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ta’aziyar rasuwar mahaifinsa — Galadiman Kano, Abbas Sunusi.
Shin Mataimakin Gwamnan Bauchi ya ‘mari’ Ministan Tinubu? An shiga ruɗani kan satar al’aurar maza a ƙasar ChadiShettima ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai, yana mai bayyana Kano a matsayin madubin Arewacin Nijeriya.
Yayin da yake nanata muhimmancin zaman lafiya, ya bayyana cewa kada a yi sake da Kano, inda ya buga misali da yadda rashin zaman lafiya ya ɗaiɗaita Jihar Borno.
Shettima ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a fannin siyasa da su ajiye banbancin aƙidu, su bai wa ci gaban Kano fifiko a kan komai.
Ya tunatar da cewa Jihar Kano wata cibiya da kusan duk jihohin Arewa suka kewaye kuma ta zama tamkar wata ƙofa da ta zama mahaɗar jihohin
“Idan za ka je Borno ko Bauchi ko Sakkwato, dole ne sai ka bi ta Kano. Saboda haka Kano jiha ce ta kowa.
Aminiya ta ruwaito cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya yi Mataimakin Shugaban Ƙasar rakiya a yayin ziyarar ta’aziyyar da ya kai gidan marigayi Galadiman Kano.