HausaTv:
2025-04-19@13:02:29 GMT

Nijar : An nada Janar Tiani, a mukamin shugaban rikon kwarya

Published: 27th, March 2025 GMT

A Jamhuriyar Nijar, an daga martabar Abdourahmane Tiani madugun juyin mulkin sojin kasar daga mukamin Birgediya Janar zuwa Janar, mukamin soji mafi girma a kasar.

An ba Abdourahmane Tiani wannan mukamin ne bayan tabbatar masa da mukamin shugaban rikon kwarya na kasar a bikin da aka gudanar a jiya Laraba a Yamai babban birrin kasar.

Kafin hakan kuma Janar Abdourahamane Tiani, ya sa hannu kan dokar tsarin mulki na wucin gadi, mai taken “Tsarin farfado da Nijar”.

Bisa wannan doka, Tiani zai jagoranci kasar tsawon shekaru 5 tun daga ranar kaddamar da dokar, yayin da ainihin wa’adinta zai danganta da halin tsaro, da bukatun farfadowar kasar, da kuma ajandar kawancen kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso.

Hukumomin wucin gadin sun kunshi shugaban jamhuriyar Nijar, da kwamiti mai kula da harkokin tsaron kasar, da gwamnati da kwamitin sulhu, da hukumar sa ido kan harkar jin kai da sauransu. 

Wata dokar kuma da shugaban rikon kwaryar ya sanya wa hannu a jiya ita ce ta rusa dukkanin jam’iyyun siyasa a duk fadin kasar.

An amince da wannan sabon tsarin mulki ne bisa kudurorin da aka tattara, a yayin taron farfado da kasa da aka gudanar a tsakanin ranakun 15 zuwa 19 ga watan da ya gabata a birnin Yamai, fadar mulkin kasar.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Kasar Iran Ya Ce: Iran Da Saudiyya Za Su Iya Magance Yawancin Matsalolin Yankin Gabas Ta Tsakiya

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Iran da Saudiyya za su iya magance yawancin matsalolin yankin Gabas ta tsakiya

Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran da Saudiyya za su iya magance yawancin matsalolin yankin Gabas ta Tsakiya ta hanyar dogaro da karfinsu a hade ba tare da bukatar shiga tsakani daga kasashen waje ba.

Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkian ya tarbi ministan tsaron kasar Saudiyya Khalid bin Salman a yammacin jiya Alhamis, wanda ke ziyarar aiki a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran dauke da wata babbar tawagarsa.

Shugaban na Iran ya jaddada cewa Iran ta kuduri aniyar karfafa alakar ‘yan uwantaka a tsakanin kasashen musulmi.

Pezeshkian ta kara da cewa: Saboda wata wasiyya ta hadin gwiwa, shugabannin kasashen musulmi za su iya ba da misali mai kyau na zaman tare da samun bunkasar wadata.

Shugaban na Iran ya ci gaba da cewa: Iran a shirye take ta fadada alakar ta da Saudiyya ta kowane fanni.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Watsi Da Zargin Takurawa Mataimakin Shugaban Kasa Shettima
  • Dokar-ta-baci: Shugaban Majalisar Wakilai Ya Gargadi Kantoman Ribas
  • Shugaban Kasar Iran Ya Ce: Iran Da Saudiyya Za Su Iya Magance Yawancin Matsalolin Yankin Gabas Ta Tsakiya
  • Neja Za Ta Kaddamar da Ayyukan Jiragen Sama Daga Filin Jirgin Sama na Bola Ahmed Tinubu.
  • Bukatar Kawo Karshen Mamayar Da Kamaru Ke Yi Wa Yankunan Nijeriya
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Makasudin Rubuta Sakon Jagora Ga Shugaban Kasar Rasha
  • Kasar Pakistan Ta Kara Jaddada Dokar Rashin Amincewa Da HKI A Matsayi Kasa
  • MDD Ta Nuna Damuwarta Akan Kokarin Sake Raba Kasar Sudan Gida Biyu
  • Najeriya da gwamnatin sojin Nijar sun sasanta
  • Ministan harkokin wajen Najeriya Ya kai ziyara Nijar