NLC a Zamfara sun Bada Wa’adin Kwanaki 14 a Aiwatar da Mafi Karancin Albashi
Published: 27th, March 2025 GMT
Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC a jihar Zamfara sun bayar da wa’adin kwanaki 14 ga gwamnatin jihar, inda suka bukaci da a kawo karshen kura-kuran da aka samu wajen aiwatar da mafi karancin albashi na N70,000.
An sanar da wa’adin ne a wani taron manema labarai a Gusau bayan wani taron gaggawa da kungiyoyin kwadago suka yi.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kungiyar NLC na jihar Zamfara, Malam Sani Halliru, ya bayyana rashin jituwar da ake samu wajen biyan albashin watan Maris a matsayin abin bakin ciki da damuwa ga ma’aikatan gwamnati.
“Ya zama dole mu kira wannan taron manema labarai saboda mun ji takaicin yadda gwamnatin jihar ke aiwatar da mafi karancin albashi,” in ji Halliru.
Ya kara da cewa tun da farko gwamnatin jihar ta kafa kwamitin da zai sa ido a kan yadda za a aiwatar da sabon albashin tare da tabbatar wa ma’aikata cewa za a fara aiki a watan Maris. Sai dai ya lura cewa albashin watan Maris da aka biya a baya-bayan nan ya gaza yadda ake tsammani.
“Wasu ma’aikata sun samu karin Naira 3,000 kacal, yayin da wasu suka samu N4,000, N5,000, ko kuma akalla Naira 7,000. Har ma fiye da haka, an cire wasu ma’aikatan ba bisa ka’ida ba daga cikin albashin ma’aikata.” Ya kara da cewa.
Malam Sani Haliru ya kuma bayyana lamarin a matsayin cin amana, ya kuma yi gargadin cewa, idan gwamnati ta gaza magance wadannan matsalolin nan da makonni biyu, kungiyoyin za su dauki mataki.
Shi ma da yake jawabi, Shugaban TUC, Sa’idu Mudi, ya koka kan yadda har yanzu Zamfara ce jiha daya tilo da ba ta fara aiwatar da mafi karancin albashi na N70,000.
“Dukkan shugabannin kwadago da ma’aikata a jihar sun ji takaicin gazawar gwamnati wajen cika alkawarin da ta dauka.
A cewar Mudi sun ji takaicin kwamitin da aka nada domin aiwatar da sabon albashin yaki yin aikin da ya dace.
Ya yi zargin cewa da gangan wasu mutane a cikin gwamnati ke yin zagon kasa wajen aiwatar da aikin tare da yin kira ga Gwamna Dauda Lawal da ya kaddamar da bincike kan lamarin tare da daukar matakin da ya dace.
COV/AMINU DALHATU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kaduna Ta Jadadda Kudurin Ta Wajen Samarda Tsaftatacen Ruwan Sha Ga Al’umma
Ma’aikatar Ayyuka da Samar da Kayayyakin More Rayuwa, tare da hadin gwiwar First Impression Communication Limited, ta shirya wani taro kan shirin Samar da Ruwa Mai Tsafta a Birane da Karkara da Tsabtace Muhalli da Kiwon Lafiya (SURWASH) da ya gudana a Arewa House, a Kaduna.
Da yake bude taron, Kwamishinan Ayyuka da Samar da Kayayyakin More Rayuwa, Dakta Ibrahim Hamza, ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na magance matsalar karancin ruwa a jihar.
Kwamshinan wanda Mataimakin Daraktan Albarkatun Ruwa, David Roven Aliyu ya wakilta, ya bayyana kokarin da gwamnati ke yi, ciki har da gina rijiyoyin burtsatse a wasu al’ummomi domin inganta tsaftar muhalli da kiwon lafiya.
“Shirin SURWASH na Najeriya wani shiri ne da Asusun Bada Lamuni na Duniya (World Bank) ke daukar nauyinsa da dala miliyan 700 domin inganta ayyukan WASH a jihohi bakwai na Najeriya, ciki har da Kaduna.
Manufar shirin ita ce samar da ruwan sha mai tsafta ga mutane miliyan shida da kuma inganta tsaftar muhalli ga mutane miliyan 1.4.
Dakta Hamza ya bayyana cewa an ware kananan hukumomi guda shida a Jihar Kaduna wanda suka hada da —Soba, Igabi, Chikun, Jaba, Jema’a, da Sabon Gari—domin tabbatar da su sun samu tsaftatacen Ruwa Sha a yankunan su.
“Da zarar wadannan yankuna sun cika ka’idojin da ake bukata, za a kara zabar karin kananan hukumomi guda bakwai domin shirin,” in ji shi.
Ya bukaci jama’a su kare kayayyakin tsafta da kiwon lafiya da gwamnati ta samar domin su dade ana amfana da su.
A nasa jawabin, Shugaban Shirin SURWASH na Kaduna, Mista Esau Ambinjah, ya jaddada muhimmancin hadin gwiwar al’umma wajen kare rijiyoyin burtsatse da sauran kayayyakin tsafta.
Ya kuma bayyana cewa an riga an zabi kananan hukumomi guda bakwai—Sanga, Makarfi, Kudan, Zaria, Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Kudu, da Zangon Kataf—domin shirin SURWASH.
A nata jawabin, Shugabar Kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN), Amira Hafsatu Musa Isa, ta bada shawarar cewa ya kamata a sanya abun da ya dace da al’adu da addini a cikin shirye-shiryen wayar da kai.
Haka kuma, Shugabar Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen mata a Kaduna, Bishop Eister Yawai, ta bukaci a fadada yakin wayar da kan SURWASH zuwa wuraren addinai.
Ta bayyana cewa samun tsaftataccen ruwa yana da matukar muhimmanci wajen hana yaduwar cututtukan da ke da nasaba da ruwa.
Ta kuma bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su kara kaimi wajen magance matsalar karancin ruwa a wasu al’umomi.
Wanda ya gabatar da shirin, Yusuf Idris, ya gabatar da sanarwar wayar da kai na SURWASH da aka fassara cikin Hausa da turanci, inda mahalarta suka gabatar da ra’ayoyinsu domin inganta shirin.
Cov/Adamu Yusuf