Kwara Ta Gargadi Jama’a Akan Gine-Gine Akan Bututun Ruwa
Published: 27th, March 2025 GMT
Gwamnatin jihar Kwara ta gargadi mazauna jihar kan yin gine-gine a kan bututun ruwa a fadin jihar.
Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar, Usman Yunusa Lade, ya yi wannan gargadin a lokacin da ya kai ziyarar duba aikin gyaran babban bututun ruwa dake Flower Garden, a Ilorin.
Kwamishinan, wanda ya samu wakilcin Sakatariyar Dindindin, Misis Christiana Asonibare, ta ce “kamar gine-gine, masallatai, coci-coci da shaguna a kan bututun ruwa da jama’a ke yi yana da illa ga samar da isasshen ruwa a fadin jihar.
Yunusa -Lade ya yi kira ga daukacin mazauna yankin da su kara kaimi ga kokarin gwamnati ta hanyar yin la’akari da bututun ruwa kafin a gina wani gini domin kaucewa lalata bututun ruwa da hana ruwa gudu ga al’umma.
A nasa bangaren babban Injiniya mai kula da aikin gyaran bututun da aka gyara a lambun Flower, Bamidele Idowu, ya tabbatar da cewa an kammala gyaran kuma za a gudanar da gwajin domin tabbatar da cewa ba a samu matsala ba.
Idowu ya bada tabbacin cewa yankunan da suka hada da Flower Garden, Lajorin, Offa Road, Sabo-Oke, Amilengbe, Adualere, Isale-koko, Oja-Gboro, da Ipata da dai sauransu za su ci gajiyar kammala gyaran da zarar an fara aikin turo ruwa.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwara Ruwa bututun ruwa
এছাড়াও পড়ুন:
Siriya : Ofishin jakadancin Amurka ya yi gargadi game da yiyuwar hare-hare a yayin bikin sallah
Ofishin jakadancin Amurka da ke Damascus ya fitar da wata sanarwar gaggawa, inda ya yi kira ga daukacin Amurkawa da su gaggauta ficewa daga kasar Syria, sakamakon karuwar hare-haren da ake kai wa a lokacin bukukuwan sallar Idi, wanda ke kawo karshen azumin watan Ramadan mai alfarma.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta daukaka tafiye-tafiye zuwa Syria zuwa mataki na 4 mafi girman inda aka gargadi, Amurkawa da kada su je kasar Siriya bisa kowane dalili.
Ofishin jakadancin ya gargadi ‘yan kasar game da yiwuwar kai hari kan “ofisoshin jakadanci, kungiyoyin kasa da kasa da cibiyoyin jama’a na Syria” a Damascus.
Halin tsaro a Syria ya tabarbare bayan da kungiyoyin ‘yan ta’adda, karkashin jagorancin Hay’at Tahrir al-Sham, suka hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad a ranar 8 ga Disamba, 2024.
Tun bayan rugujewar gwamnatin Assad, sojojin Isra’ila ke kai hare-hare ta sama a kan cibiyoyin soji, da kuma rumbun adana kayan yaki na sojojin Siriya.