Aminiya:
2025-04-19@17:20:42 GMT

Lakurawa sun kashe jami’an Kwastam 2 a Kebbi

Published: 27th, March 2025 GMT

Wasu ’yan bindiga da ake zargin Lakurawa ne, sun kai har iyakar Bachaka da ke Ƙaramar Hukumar Argungu a Jihar Kebbi, inda suka kashe jami’an Kwastam biyu da wani mazaunin garin.

Harin ya faru ne kwana guda bayan da dakarun tsaro suka kashe wasu dakarun Lakurawa a yankin.

Ban sani ba ko zan tsaya takara a 2027 — Atiku Mutum 2,000 za su riƙa kamuwa da cutar HIV duk rana a duniya — MDD

Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi, ta tabbatar da faruwar harin, inda ta ce ba a tantance sunayen jami’an Kwastam da aka kashe ba.

“Eh, an kai hari, kuma ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an Kwastam biyu da wani mazaunin Bachaka,” in ji kakakin rundunar, Nafiu Abubakar.

Bayan harin, Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Sani Bello, ya ziyarci wajen tare da tabbatar wa jama’a cewa hukumomin tsaro na aiki domin kama waɗanda suka kai harin.

“Waɗannan hare-hare na nuni da cewa miyagun suna raguwa saboda yawan farmakin da muke kai musu.

“Za mu ci gaba da yaƙar su har sai mun kawar da su gaba ɗaya,” in ji CP Bello.

Har yanzu, jama’a na cikin fargaba game da tsaro a yankunan kan iyaka, yayin da suke nuna damuwa kan yiwuwar sake kai musu hare-hare.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Kwastam Lakurawa jami an Kwastam

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan sanda sun ceto ɗalibai 10 sun kashe ɗan bindiga a Edo

Jami’an rundunar ’yan sandan jihar Edo sun ceto ɗalibai 10 da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Edo.

An kashe ɗaya daga cikin ’yan bindigan, a yayin musayar wuta da ’yan sanda a lokacin aikin ceto, yayin da sauran suka tsere da raunukan harbi.

Daily Trust ta ruwaito cewa an yi garkuwa da ɗaliban ne a ranar 16 ga Afrilu, 2025, a kan hanyarsu ta zuwa Jami’ar Babcock don taron shekara-shekara na GYC Africa.

Kakakin rundunar, SP Kontongs Bello, wanda ya tabbatar da ceton, ya ce da samu rahoton sace daliban, kwamishinan ’yan sandan jihar, Funsho Adegboye, ya tura ’yan sanda na musamman tare da ’yan banga da maharba cikin daji domin ceto su da kuma kama waɗanda ake zargi.

Ana kashe ’yan Najeriya amma Tinubu ya fi damuwa da Zaɓen 2027 — SDP Makarantar Bare: Shekara 20 dalibai na karatu a matsanancin yanayi

Ya ce a lokacin aikin, an kashe ɗaya daga cikin ’yan garkuwan, yayin da sauran suka tsere da raunukan harsashi.
“Jami’an sun yi taka-tsan-tsan don guje wa asarar rayukan fararen hula saboda ’yan garkuwan sun yi amfani da waɗanda aka sace a matsayin garkuwa.”

A cewarsa, wani Sufeton ɗan sanda ya samu raunin harbin bindiga a lokacin aikin, kuma yana samun kulawa a asibiti a halin yanzu.

Ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin cafke ‘yan garkuwan da suka tsere.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan sanda sun ceto ɗalibai 10 sun kashe ɗan bindiga a Edo
  • Amurka Ta Kaddamar Da Sabbin Hare-Hare Kan Garuruwan Sana’a, Sa’adah Da Al-Jawf Na Kasar Yemen
  • ‘Yan Sandan Sun Ceto Wasu Mutane Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara
  • An kashe sojoji, fararen hula da dama a Borno
  • Amurka Ta Kashe Mutane 38 Tare Da Jikkata Fiye Da 100 A Harin Da Ta Kai Lardin Al-Hudaidah Na Yemen
  • Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe Ta Bada Tabbacin Tsaro A Bukin Ista
  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda a Sambisa da Kudancin Tumbun
  • Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kona Yara Da Mata A Harin Da Suka Kai Khum Yunis Na Gaza
  •  Sojojin HKI Suna Ci Gaba Da Kai Hare-hare A Kudancin Lebanon
  • An Kashe Shanu 36, an ba 42 guba a Filato