Isra’ila : An yi zanga zangar adawa da gwamnatin Netanyahu a Tel-Aviv
Published: 27th, March 2025 GMT
A Isra’ila dubban masu zanga-zanga ne suka taru a Tel Aviv domin nuna adawa da mulkin firaministan kasar Benjamin Netanyahu.
Masu zanga zangar sun kuma bukaci a tsagaita bude wuta da kuma sako fursunonin da ake tsare da su a Gaza.
Sun rike alluna masu dauke da hotunan wadanda ake tsare da su a Gaza ko kuma allunan neman tsagaita bude wuta da Hamas cikin gaggawa.
Gamayyar kungiyoyin da ke adawa da shugaban majalisar ministocin ne suka shirya zanga-zangar da ta barke a makon da ya gabata, wanda suke zarginsa da matakin korar shugaban hukumar liken asiri ta cikin gida wato Shin Bet, Ronen Bar.
Wata Kuri’ar jin ra’ayin jama’a a isra’ila ta nuna cewa yawancin ‘yan Isra’ila na adawa da kawo karshen yarjejeniyar tsagaita bude wuta inda suke son ci gaba da tattaunawa da Hamas.
Kungiyar Hamas ta sake nanata cewa za a iya kashe mutanen da suka yi garkuwa da su idan Isra’ila ta yi kokarin kwato su da karfin tsiya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kashe Matafiya: Gwamnatin Kano Ta Aika Tawaga Zuwa Edo
Bugu da kari, tawagar za ta gana da shugabannin al’ummar Hausawa na jihar domin tattauna lamarin tare da bayar da shawarwarin da suka dace.
Sanarwar ta bukaci ‘yan jihar da su kwantar da hankalinsu tare da kaucewa duk wani abu da zai iya haifar da tarzoma, tare da tabbatar wa jama’a cewa, ana daukar matakan da suka dace na diflomasiyya da na shari’a don magance lamarin yadda ya kamata.
Gwamnatin jihar Kano ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda lamarin ya shafa tare da yin addu’ar Allah ya jikansu da rahama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp